Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC

Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin baiwa dukkan yan Najeriya mitan wutan lantarki domin kawar da tsarin da ake kai yanzu na raba 'Bill' na kiyasi.

A takardar da aka saki ranar Laraba, shugaban hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), James Momoh, ya ce hakazalika shugaba Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan.

Amma Momoh yace za'a togaciye "Talakawan" Najeriya daga karin farashin da za'ayi.

Shugaban NERC ya ce karin kudin ba zai shafi wadanda ake rabawa 'Bill' na kiyasi ba har yanzu har sai sun samu mita.

"Hukumar NERC na son bayyanawa yan Najeriya cewa karin farashin wutan lantarkin da za'ayi yanzu zai bi ka'ida. Daga cikin ka'idojin shine sai an tattauna da mutum kan adadin wutan lantarkin sa'o'in da yake bukata a rana." Momoh yace

"A gaba daya tsarin da za;ayi, ba zai shafi talakawan Najeriya ba."

"Hakan na nufin cewa kwastomomi maras mita ba zasu samu karin farashi ba fiye da wanda masu mita suke samu. Bugu da kari, ba za'a canza farashin da yawancin talakawan Najeriya ke biya ba masu shan wutan 50W ko kasa da haka."

"Mutane masu samun wuta kasa da awanni 12 a rana ba zasu fuskanci karin farashi ba."

Buhari ya bada umurnin kada farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC
Buhari ya bada umurnin kada farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC
Asali: Twitter

Zaku tuna cewa a watan Junairu, hukumar NERC ta sanarwa yan Najeriya cewa za'a kara farashin wutan lantarki daga watan Afrilu.

Amma aka dakatar da yin hakan saboda bullar annobar Korona a watan Maris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng