Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta mana tsegumi - Kamfanin Intels ga Atiku
- Kamfanin Intels ta musanta ikirarin babban mai hannun jarinta, Atiku Abubakar
- A ranar Litinin, Atiku ya janye kudinsa daga kamfanin saboda tsangwamar da gwamnatin Buhari ke masa, a cewarsa
- Har yanzu gwamnatin Buhari ba tayi tsokaci kan ikirarin Atiku ba
Kamfanin Integrated Logistics Services Limited (Intels) ya bayyana cewa ko kadan siyasar mulkin shugaba Buhari ba ta shafi harkokin kasuwancinsa ba.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ranar Litinin, ya sanar da cewa ya sayar da hannun jarinsa dake kamfanin Intels.
Atiku, wanda tare da shi aka kafa kamfanin ya ce an tilasta masa sayar da hannun jarinsa dake cikin kamfanin saboda irin musgunawar da gwamnatin Buhari ke masa tun shekarar 2015.
Amma jawabin da mai magana da yawun kamfanin Intels, Tommaso Ruffinoni, ya saki, ya ce kamfanin ba ta fuskantar wani matsala.
Kamfanin ya ce Atiku ya sayar da hannun jarinsa ne bisa dalilai na rashin fahimtar juna tsakaninsa da sabbin shugabannin kamfanin.
"Intel Nigeria Limited da uwar kamfanin, Orlean Invest Holding, na karyata rahotannin dake yawo a jiya da yau cewa kasuwancinsu na fuskantan tsangwama daga gwamnatin tarayya," jawabin yace.
"Dauke kamfanin daga duniyar Atiku Abubakar shawarace ta tattalin arzikin kamfanin, da kuma rashin fahimtar juna tsakaninsa da sabbin shugabannin kamfanin Intels – Orlean."
KU DUBA: Karya ne, bamu kara farashin wutan lantarki ba, hukumar NERC
KU KARANTA: Ba mu na niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed
A wani labarin kuwa, sama da ma'aikatan kamfanin INTELS 700 da aka sallama sun yi zanga-zanga, suna neman hakkinsu.
Ma'aikatan da aka kora sun fara zanga-zangan tun ranan Talata kuma sun ce ba zasu daina ba har sai an biyasu hakkinsu, Vanguard ta ruwaito.
Masu zanga-zangan wadanda mambobin kungiyar ma'aikatan tashohon jirgin ruwa ne AMS, sun tare kofar shiga kamfanin rike da takardu masu rubuce-rubuce a kai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng