Albashi mafi karanci: 'Yan sanda sun baɗawa masu zanga-zanga barkonun tsohuwa a Filato

Albashi mafi karanci: 'Yan sanda sun baɗawa masu zanga-zanga barkonun tsohuwa a Filato

- Jami'an tsaro sun tarwatsa zanga zangan da ma'aikatan kananan hukumomi a Jihar Plateau ke yi a Jos tare da kama 32 cikinsu

- Ma'aikatan na zanga zangan ne kan cewa gwamnatin jihar ta ki biyansu albashi mafi karanci na naira dubu talatin

- Hukumar 'yan sandan jihar ta ce bata da masaniya cewa jami'anta sun kama wani sai dai sun tafi wurin zanga-zangan ne domin tabbatar da cewa ba a tada fitina ba

Hadakar jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji sun bada wa ma'aikatan kananan hukumomi da ke zanga zanga a Jihar Filato barkonon tsohuwa, The Punch ta ruwaito.

Ma'aikatan daga kananan hukumomi bakwai na jihar sun kwashe makonni uku suna zanga zanga kan rashin biyansu albashi mafi karanci na N30,000 da gwamnatin jihar ta gaza yi.

Albashi mafi karanci: 'Yan sanda sun badawa masu zanga zanga barkonun tsohuwa a Filato
Albashi mafi karanci: 'Yan sanda sun badawa masu zanga zanga barkonun tsohuwa a Filato. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramatawa mutum 100 fita kasashen waje, ta fitar da bayanan fasfo dinsu

An gano cewa ma'aikatan kananan hukumomin da suka sanya bakaken tufafi sun taru a gaban sakatariyar Jihar a Jos a ranar Litinin tun karfe 7 na safe don cigaba da zanga zanga da suka saba amma sai jami'an tsaro suka zo suka tarwatsa su da borkonon tsohuwa.

Mataimakin shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi na karamar hukumar Bokkos, Barnabas Philips, ya shaidawa The Punch a ranar Litinin a Jos cewa jami'an tsaro sun kama mambobinsu 32 sun tafi da su hedkwatan hukumar cigaban birnin Jos yayinda saura na kokarin tserewa kuma wasu sun jikkata.

KU KARANTA: Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Philip, daya daga cikin wadanda aka kama ya yi tir da abinda gwamnatin jihar ta yi inda yace, "A yanzu da nake maka magana, muna hedkwatan JMDB a Jos bayan gwamnati ta turo 'yan sanda da sojoji su bada mana borkonon tsohuwa su kuma kama ma'aikatan kananan hukumomi saboda zanga zangan rashin biyan mu albashi mafi karanci na N30,000.

"An kama ma'aikatan kananan hukumomi 32 ciki har da ni da safen nan kawai don muna neman hakkin mu.

"Sun saka mu cikin motocci sun kawo mu nan. Allah wadai da wannan abin."

Da aka tuntube shi, Kakakin yan sandan jihar, Ubah Ogaba ya ce bai da masaniya kan cewa jami'ansu sun kama wasu saboda zanga zanga.

Ogbah ya ce, "Ban san cewa an kama wani ma'aikacin karamar hukuma ba. Da muka gano wasu na neman tada fitina a jihar, sun tura jami'an mu don su tabbatar hakan bai faru ba, abinda yasa muka tura jami'an mu sakatariya kenan."

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel