COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramatawa mutum 100 fita kasashen waje, ta fitar da bayanan fasfo dinsu

COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramatawa mutum 100 fita kasashen waje, ta fitar da bayanan fasfo dinsu

- Gwamnatin tarayya na cigaba da ƙara ƙaimi don ganin ta daƙile yaɗuwar cutar korona

- Don haka ta hukunta wasu fasinjoji 100 da suka shigo Najeriya amma basu yi gwajin COVID-19 da aka wajabta ba

- Ta haramta wa wadannan fasinjojin 100 fita daga Najeriya na tsawon watanni shida

An saka wa wasu fasinjoji 100 takunkumin hana fita ƙasar waje saboda sun ƙi zuwa yin gwajin korona da aka wajabtawa waɗanda suka dawo Najeriya.

Ana yin gwajin ne bayan wa'adin kwanaki 7 na killacewa da ake wajabtawa waɗanda suka shigo kasar.

Kwamitin shugaban kasa na yaki da korona, PTF, ta fitar da jerin lambobin fasfo ɗin wadanda suka saba dokar duk da cewa ba a bayyana sunayensu ba.

COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramatawa mutum 100 fita kasashen waje, ta fitar da bayanan fasfo din su
COVID-19: Gwamnatin Najeriya ta haramatawa mutum 100 fita kasashen waje, ta fitar da bayanan fasfo din su. Hoto: @TheNationNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Wani sako da ta wallafa ta shafin ta na Twitter a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu ya ce, "PTF ta saka takunkumin hana fita ƙasar waje kan wasu fasinjoji 100 da suka ƙi yin gwajin korona da aka wajabta wa wadanda suka shigo kasar bayan kwanaki 7."

Hakan na nufin cewa nan da watanni shida, fasinjojin da abin ya shafa ba za su iya fita daga Najeriya zuwa kasashen waje ba.

An tuntubi mutane 100 da abin ya shafa kuma sun tabbatar cewa ba suyi gwajin da ake yi bayan dawowa ƙasar ba.

KU KARANTA: Mahara sun yanka wani mafarauci a Abuja

Wani babban majiya daga PTF wanda ya yi magana da The Nation ya bayyana cewa an aike wa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) da sauran hukumomin tsaro sunayen wadanda aka haramtawa fita ƙasar don su hana su fita.

A cewar majiyar, za a soke fasfo ɗin su baki ɗaya idan aka sake samunsu da aikata wani laifi.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel