An sace matan aure biyu, an kashe mutane 18 a Kaduna

An sace matan aure biyu, an kashe mutane 18 a Kaduna

- Wasu 'yan bindiga sun kai wasu jerin hare-hare a yankin karamar Giwa da ke jihar Kaduna

- Kwamishinan harkokin tsaron cikin gida a Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an fara kai hare-haren ne ranar sabuwar shekara

- Kazalika, wasu 'yan bindigar sun kashe wani babban limami saboda yawan sukarsu a hudubarsa

Kimanin mutum 18 ake zargin mahara sun kashe tare da sace wasu matan aure biyu yayin wasu jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa, Kwamishinan al'amurran cikin gida da sha'anin tsaro, Samuel Aruwa, ya ce farmakin ya faru ne a ƙauyukan Kaya dake da iyaka da Hayin Kaura ta jihar Katsina, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A cewar Kwamishinan, an fara kai hare haren ne tun ranar juma'a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, ya kara da cewa cikin waɗanda maharan suka sace harda wata matar aure.

KARANTA: Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023

Da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin asabar ne kuma, wasu mahaya babura sama da su 50 ɗauke da mutum 3 tare da bindiga ƙirar AK-47, suka shiga ƙauyen na Kaya suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi.

"Rikicin ya faro tun 1 ga watan Janairun 2021 lokacin da maharan suka farwa ƙauyen Kaya, suka kashe tare da sace mutanen garin ciki harda wata matar aure" in ji Samuel Aruwa.

An sace matan aure biyu, an kashe mutane 18 a Kaduna
An sace matan aure biyu, an kashe mutane 18 a Kaduna @Thecableng
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa, "Maharan sun fuskanci mummunar turjiya daga yan sa kai na Kaya, da kuma wasu daga Hayin Kaura dake jihar Katsina a ƙoƙarinsu na inganta tsaro a yankunansu."

KARANTA: Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

Ya ce, an rasa rayuka da dama amma dai rundunar sojin Najeriya haɗin gwiwa da ta yan sanda, sun yi kokari wajen aike da dakaru cikin gaggawa yankin tare da jirgin sojin sama.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa 'yan bindiga a jihar Kaduna sun kashe babban limamin kauyen Kwaran Rafi a karamar hukumar Igabi.

Muryar marigayi, babban limanmin kauyen, Danleeman Isah, ta yi fice wajen suka da Alla-wadai da ayyukan 'yan bindiga.

Kazalika, wasu 'yan bindigar sun kashe sarkin yakin Godogodo da wasu sauran mutane a Jema'a da Kajuru.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel