Sanata Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023

Sanata Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023

- Malam Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce babu tsarin kama-kama a mulkin kasa a kundin tsarin mulkin APC

- Tsohon gwamnan kuma sanatan Kano ta tsakiya ya ce cancanta ce ya kamata ta zama abar dubawa a zaben gaba

- Shekarau ya yi tsokaci akan alakar da ke tsakaninsa da gwaman Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon gwamna Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu wani tsarin karɓa-karɓa a kundin tsarin gudanarwa na jami'iyyar APC.

Sanatan, ya yi kira da masu kaɗa ƙuri'a da su mayar da hankalinsu kan ɗan takarar da ya cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

A cewar Malam Shekarau, ingancin ɗan takara shine ya kamata ya zama muhimmin abin dubawa a zaɓe mai zuwa, ya ƙara da cewa babu wani tsarin karɓa-karɓa cikin jam'iyyar APC face kawai tunani ne da mutane suke ganin hakan ya dace.

KARANTA: Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani

"Ina so na gaya muku cewa a kundin gudanarwa na APC, babu wurin da aka ambaci maganar bayar da mulki na shiyya-shiyya. Ina ga dai jam'iyyar PDP ce kawai ke da wannan tunanin.

"Abinda kawai muka sani shine ingancin shugabanci da adalci tare da tafiya da kowa; wannan shine kawai." In ji Shekarau.

Sanata Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023
Sanata Shekarau ya ce babu karba-karba a tsarin APC, ya bawa 'yan Nigeria shawara akan zaben 2023 @Daily_trust
Asali: Twitter

Bugu da ƙari, Shekarau ya jaddada cewa alaƙarsa da tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso, da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na nan kalau.

KARANTA: Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon suna

Ya ce, "Ni da Ganduje muna tare tsawon shekaru. Lokacin ina famanat sakatare shi kuma lokacin yana Kwamishina, tun can muna mu'amala tare.

"Haka abin yake ni da Kwankwaso; bambancin siyasar mu bai shafi alaƙar mu ba ko kaɗan kuma ban taɓa barin wata jam'iyya zuwa wata ba saboda shi" cewar Malam Ibrahim Shekarau.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon sanata, Kwamred Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya zai shiryawa kafin ya shiga siyasa.

Sanata Shehu Sani ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata na shekarar 2019 baya hamayyarsa da gwamna El-Rufa'i ta tilasta shi barin APC.

A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya neme ya ba shi kafin ya tsunduma siyasa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel