Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

- Shekarar 2020 ta zo cike da abubuwa masu ban mamaki a bangarori daban-daban da suka hada da na siyasa

- Daga massasarar tattalin arziki zuwa rashin tsaro da ya laƙume rayuwa zuwa siyasa inda kowanne ke burin ganin shi ya kai labari.

- A ɓangaren siyasa, mun zaƙulo abubuwan da suka faru kuma suka shiga tarihin siyasar Najeriya, kamar yadda Vanguard ta rawaito

1. Sauke Oshiomhole daga shugabancin APC da rikicinsa da Obaseki

Duk da cewa rigimar shugabancin jam'iyyar APC da Oshiomhole ke yi, ya faro tun Disamba 2019 inda wasu shugabannin jam'iyyar a matakin mazaɓu suka sanar da dakatar da shi, tsohon shugaban ya cigaba jagorancin jam'iyyar har 4 ga watan Maris lokacin da babbar kotun Abuja ta tabbatar da dakatarwar.

A 25 ga Yuni ne kwamitin zartarwa na jam'iyyar ya ruguje shugabancin tsagin Oshiomhole. Rugujewar da ta baiwa Gov. Mai Mala shugabancin riƙo jam'iyyar.

Ana ganin Gwamnan Edo, Mr Godwin Obaseki ne kanwa uwar gamin dakatar da Oshiomhole. Da rikici ya ƙi karewa, Obaseki ya bar jam'iyyar ya karbi tikiti a PDP don tsayawa takarar gwamna.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama kwararrun matasan barayin mota hudu, sunayensu

Ana yiwa zaben Gwamna a Edon kallon zakaran gwaji kan zaɓe mai zuwa na 2023, ana ganin kamar zaɓe ne tsakanin masoya da masu adawa da Tinubu.

Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020
Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020 @OfficialAPC
Asali: Twitter

2. Sake naɗa shugaban hukumar zabe

An sake naɗa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban Hukumar zaben ran 27, 2020. Tun 1999 babu wani shugaban hukumar da aka sake mayar da shi muƙamin shugabancin wannan hukumar.

Wannan naɗi ya fuskanci martani mai zafi daga yan Najeriya da wasu yan siyasa.

KARANTA: Sa hannu akan kasafin kudin 2021: Buhari ya gargadi rukunin wasu hukumomi da ma'aikatun FG

3. Sauya Shekar Gwamna Dave Umahi

Lokacin da gwamnan jihar Ebonyi ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC cikin watan Nuwamba 17, ya zama batun tattaunawa a ko'ina da ma kafafen sada zumunta.

Ana ganin canza shekar tashi, bata rasa nasaba da yana yunkurin neman kujerar shugabancin ƙasar ne.

4. Rikicin Bala Muhammad da Yakubu Dogara

2020 shekara ce da gwamnan jihar Bauchi ya samu sabani da babban amininsa, Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai

Rikicin ya tilastawa Dogara barin jam'iyyar PDP ya koma tsohuwar jam'iyyarsa ta APC.

Cikin shekarar ne dai aka kama Obadiah Mailafiya, mai ritaya, tsohon ɗan takarar shugabancin kasar, lamarin da wasu ke masa kallon saboda addinin sa ne.

5. Sanata Abbo ya koma APC

Matashin sanata, Ishaku Abbo, wanda aka zaba a karkashin tutar inuwar Jam'iyyar PDP ya sauya sheka zuwa Jam'iyyar APC tare da bayyana cewa ya bar PDP ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan kasafin kudin sabuwar shekarar 2021

A jawabin da ya gabatar yayin saka hannu a kan kasafin kudin, shugaba Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun tarayya da ke tattara kudaden haraji.

Buhari ya ce zai dauki mataki tare da saka takunkumi akan shugabannin hukumomi da ma'aikatun da suka gaza sauke nayin da gwamnati ta dora musu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel