Sa hannu akan kasafin kudin 2021: Buhari ya gargadi wasu hukumomi da ma'aikatun FG

Sa hannu akan kasafin kudin 2021: Buhari ya gargadi wasu hukumomi da ma'aikatun FG

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan kasafin kudin sabuwar shekarar 2021

- A jawabin da ya gabatar yayin saka hannu a kan kasafin kudin, shugaba Buhari ya ja kunnen hukumomi da ma'aikatun da ke tattara haraji

- Buhari ya ce zai dauki mataki tare da saka takunkumi akan shugabannin hukumomi da ma'aikatun da suka gaza sauke nayinsu

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ja kunnen ma'aikatu da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da ke tattara haraji da su tashi tsaye don ganin sun samar da isassun kuɗaɗen shiga.

Mataimakiyar shugaba ta musamman kan shafukan sadarwa ga shugaba Buhari, Lauretta Onochie, ce ta bayyana cewa, shugaban ya fitar da wannan gargadin ne yau 31 ga watan Disambar lokacin da ya ke rattaba hannu kan kasafin kudin shekara 2021 mai kamawa.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama kwararrun matasan barayin mota hudu, sunayensu

Bayan sa hannu a kasafin na kimanin tiriliyan ₦13.588 wanda ya zama doka, shugaban ya ce, "Muna rubanya kokarinmu don tabbatar da mun samu isassun kuɗaɗe na kasafin 2021.

Sa hannu akan kasafin kudin 2021: Buhari ya gargadi wasu hukumomi da ma'aikatun FG
Sa hannu akan kasafin kudin 2021: Buhari ya gargadi wasu hukumomi da ma'aikatun FG
Asali: Twitter

"Wajibi ne ga hukumomi su tabbatar da burinmu na samar da danyen mai da fitar da shi ƙasashen waje.

KARANTA: An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa

"Duk shugaban da ya yi sakaci wajen sauke hakkinsa za mu ɗauki mataki mai tsauri kansa. Ina kira ga yan ƙasa da su yi ƙoƙarin biyan haraji kan lokaci," a cewar Buhari.

Buhari ya kara da cewa, "Duk da annobar COVID-19, mun yi manyan aiyuka da abubuwan da ya kamata a yaba daga kasafin kudin shekarar 2020"

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya tare da kalubalantar Buhari da shugabanni akan su daina dorawa Allah laifin rashin cigaban kasa.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng