Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa

Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa

- Zukekiyar budurwa a Facebook ta sha caccaka daga mabobin wata kungiya a kafar sada zumuntar

- Ta bukaci duk wani saurayi talaka da kada ya kuskura ya neme ta don ba za ta sassauta ba ko kadan

- Ta yi wallafarta ne bayan an yi caa a kan wata budurwa da ke neman miji mai kudi da zai kula da ita

Wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya ta sha caccaka daga mambobin wata kungiya a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

Budurwar da kanta taje tana jan kunne a kan cewa kada saurayi talakan da ya kuskura ya zo kusa da ita domin bata da ra'ayinsa.

Ta sanar da hakan jim kadan ne bayan da aka zage wata budurwa tas a wata fitacciyar kungiya a Facebook jiya saboda ta saka cigiyar hamshakin mijin da zai kula da ita yadda ya dace.

Kamar yadda ta wallafa, "Hmm, a gaskiya ba zan sassauta ba. Idan baka da kudi dan uwa, koma da baya. Kada kuma kowa ya caccake ni saboda na fadi ra'ayi na."

Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa
Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa. Hoto daga Ifeoma Ajaegbu
Source: Facebook

KU KARANTA: Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC

Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa
Ba zan iya auren talaka ba, idan baka da kudi kiyaye ni, Budurwa ga matasa. Hoto daga Ifeoma Ajaegbu
Source: Facebook

KU KARANTA: 2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga

A wani labari na daban, wasu iyalai sun shiga cikin gagarumin mamaki da annashuwa, bayan bayyanar sakamakon asibiti. Sakamakon ya nuna yadda matar ta kara samun ciki, bayan tana dauke da cikin wasu tagwaye.

Matar mai suna theblondebunny1 ta wallafa abin mamakin da ya faru da ita a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta TikTok, inda ta sanar da labarin yadda take shirin haifar jarirai 3, shekara mai zuwa.

Matar, wacce 'yar kasuwa ce, ta bayyana yadda al'amarin mai ban mamaki ya faru, wanda a likitance suke kira 'superfetation', mace ta iya daukar juna biyu sau 2 a wata daya, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel