Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin

Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin

- Wata mata ta bayyana yadda ta shiga matsanancin farin cikin bayan bayyanar sakamakon asibiti

- Sakamakon ya tabbatar da ta kara daukar cikin wani jaririn, bayan tana dauke da tagwaye a cikinta, kenan sun zama 3

- Al'amarin ya bai wa mutane da dama al'ajabi, don hakan ba kasafai yake faruwa ba, sai ga wasu kebabbun mutane

Wasu iyalai sun shiga cikin gagarumin mamaki da annashuwa, bayan bayyanar sakamakon asibiti. Sakamakon ya nuna yadda matar ta kara samun ciki, bayan tana dauke da cikin wasu tagwaye.

Matar mai suna theblondebunny1 ta wallafa abin mamakin da ya faru da ita a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta TikTok, inda ta sanar da labarin yadda take shirin haifar jarirai 3, shekara mai zuwa.

Matar, wacce 'yar kasuwa ce, ta bayyana yadda al'amarin mai ban mamaki ya faru, wanda a likitance suke kira 'superfetation', mace ta iya daukar juna biyu sau 2 a wata daya, The Nation ta wallafa.

Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin
Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar

Ta ce a ka'ida, yanayin jikin mace, da zarar ta samu juna biyu, bata iya kara daukar wani. Sai dai, hakan bai faru a gare ta ba.

"Don haka akwai yuwuwar in haifi yarana daban-daban, kila kuma su zama a rana daya," tace.

KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila

A wani labari na daban, wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumuntar zamani mai suna Ngozi ta bar mutane da abun mamaki a labarin da ta bada.

A wasu jerin wallafar da tayi, Ngozi ta bada labarin yadda rikici ya barke bayan ango ya harzuka kan cewa danginsa basu samu abincin biki ba.

Amarya ta fusata bayan angon ya yi mata ihu tare da tsawa a gaban kowa. Ta je bashi hakuri tare da yi masa bayani amma sai ya fusata ya yi mata tsawa a gaban kowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng