2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga

2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga

- Hedkwatar tsaro ta yi jan kunne da kakkausar murya ga dukkan wasu 'yan ta'adda da ke fadin kasar nan

- Manjo Janar John Enenche ya ce babu shakka sojin Najeriya za su sauya salon yaki da ta'addaci a kasar nan

- Ya sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja a kan yadda shekarar 2021 za ta kasance wa hukumar

A ranar Alhamis, hedkwatar tsaro ta ja kunnen 'yan ta'adda, 'yan bindiga , masu garkuwa da mutane da duk wasu masu aikata laifi da ke sassan kasar nan da su tuba tare da gujewa aikata laifukan kafin dakarun sojin su far musu a 2021.

Shugaban fannin yada labarai na dakarun sojin, Manjo Janar John Enenche, a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a tudu, iska da ruwa duk sun fara sauya salon yakar 'yan ta'adda da masu kai musu bayanai, The Nation ta ruwaito.

Ya ce, "Mayakan ta'addancin Boko Haram, 'yan bindiga da dukkan sauran masu laifuka gara su tuba a yayin da za mu shiga 2021. Babu shakka sakon da muke da shi ga 'yan ta'adda shine, kai tsaye kun saka hannu a tikitin mutuwarku saboda aiki ne da dole mu aiwatar.

2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga
2021: Dakarun sojin Najeriya za su sauya salon yaki da Boko Haram da 'yan bindiga. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Iko sai Allah: Matar aure dauke da cikin tagwaye ta sake samun wani cikin

"Kamar yadda aka karfafa mu, mun saka hannu a kan aikin kare kasarmu da 'yan kasan baki daya. Rayuwa za ta koma daidai ta yadda tattalin arziki da sauran rayuwa za ta dawo.

"Ga wadanda za su sauya hali kafin sabuwar shekara, muna basu damar yin hakan. Har yanzu kofofi a bude suka garesu don su tuba. Su miko kansu ga jami'an tsaron da ya dace."

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo

A wani labari na daban, Jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan. Ya ce shugaan kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.

Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.

"Rashin tsaron da ke addabar kasar nan ba tun yanzu yake ba. An gaje shi ne daga jam'iyyar PDP tun lokacin da suke mulki," mamba a kwamitin rikon kwarya na APC yace."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel