Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC

Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC

- Sanata Abba Ali, jigo a jam'iyyar APC ya yi magana aka tabarbarewar tsaro a fadin kasar nan

- Sanata ya ce babu shakka gwamnatin APC ta gaji rashin tsaro ne daga gwamnatin da ta gabata

- Ya tabbatar da cewa gwamnatin tana kokari kuma za ta cigaba da kokari a fannin tsaro

Jigon jam'iyyar APC, Sanata Abba Ali, ya yi martani a kan kara lalacewar tsaron kasar nan.

Ya ce shugaan kasa Muhammadu Buhari ya gaji wadannan matsalolin ne daga jam'iyyar PDP.

Ali, wanda ya yi magana daga Katsina, ya bayyana hakan a ranar Laraba ta wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da gidan talabijin na Chhannels TV a shirin siyasarmu a yau.

"Rashin tsaron da ke addabar kasar nan ba tun yanzu yake ba. An gaje shi ne daga jam'iyyar PDP tun lokacin da suke mulki," mamba a kwamitin rikon kwarya na APC yace.

Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC
Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi da safarar yara

“'Yan matan Chibok da aka sace a wasu watanni can, babu abinda suka yi har sai lokacin da mulkin APC yazo. Boko Haram a baya ta karbe kananan hukumomi 17 a jihar Borno.

“Gwamnatin kasar nan na iyakar kokarinta wurin tabbatar da ta tsare rayukan jama'a. Wannan gwamnatin ta yi kokari, tana yin kokari kuma za ta cigaba da kokarin ganin ta tabbatar da tsaron kasar nan."

Tuntuni Najeriya ke yaki da ta'addanci na kusan shekaru 10 bayan kisan shugaban Boko Haram, Mohammed Yusuf wanda ake zargin 'yan sanda da yin hakan a 2009.

KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya waske, ya ki bayyana inda uwargidan shugaban kasa take

A wani labari na daban, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce 'yan majalisar wakilai suna tsoron shugaba Muhammadu Buhari, shiyasa suka soke gayyatar da suka yi masa.

Sani ya yi wannan maganar ne da BBC Hausa, inda yace ya kamata shugaba Buhari ya bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

A cewarsa, babu dalilin da zai sanya a ce su gayyaci Buhari kuma su koma su canja ra'ayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel