Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo

Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayar da manyan shawarwari ga 'yan Najeriya

- Ya ce wajibi ne ayi hobbasa wurin kawo karshen tabarbarewar tsaro a kasar nan baki daya

- Obasanjo ya ce ya kamata a dage wurin yin ayyuka tukuru don kawo karshen talauci a Najeriya

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayar da sakonsa na sabuwar shekara ga 'yan Najeriya.

Ya ce lokaci ya yi da shugabannin Najeriya za su mike tsaye wurin tabbbar da sun yi gyara akan yadda tattalin arzikin kasa ya tabarbare. Obasanjo yayi wannan maganar ne a Abeokuta, jihar Ogun.

1. Ya ce wajibi ne su tsaya tsayin-daka wurin ganin sun kawo karshen rashin tsaro a Najeriya, saboda al'amarin kullum kara lalacewa yake yi, babu birni babu kauye.

Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo
Muhimman abubuwa 4 da ke kunshe a sakon sabuwar shekarar Obasanjo. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya waske, ya ki bayyana inda uwargidan shugaban kasa take

2. Ya yi kira ga gwamnati da su shiga harkar noma don tallafa wa kasa da samun cigaba a 2021. Wajibi ne a dage a gona don gudun kada 'yan Najeriya su dinga kwana da yunwa.

3. Ya kara da cewa, Najeriya tana bukatar addu'a, ta haka ne za a kawo karshen tashin hankalin da kasar nan take ciki. Sai dai ba addu'a kadai za a tsaya ba, wajibi ne a mike tsaye kuma a yi aiki tukuru. Tabbas za a samu nasarar idan aka yi hakan a 2021.

4. Ya kuma bayyana damuwarsa a kan rashin tsaro da kuma annobar COVID-19 mai kawo cikas ga tattalin arzikin kasa. Ya ce hakan ne babban kalubale, wanda ya janyo tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.

KU KARANTA: Da duminsa: Ana zargin jaruma Nafisa Abdullahi da fataucin miyagun kwayoyi da safarar yara

A wani labari na daban, Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa, ya ce lokacin yana kujerarsa, bai tabbatar da wasu daga cikin wadanda Shugaba Buhari ya nada ba, saboda bai amince da nagartarsu ba.

Saraki ya fadi hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake mayar da martani ga Momodu, mawallafin mujallar Ovation, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Momodu ya bayyana tsohon gwamnan Kwara a matsayin shugaban da yafi ko wanne shugaba kaifin tunani a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel