Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)

- A karshe, an yi lebur da gidan da aka shirya banbadewa a jihar Kaduna

- Hukumar KASUPDA ta ce an rusa gidan ne saboda sun saba dokokin da gwamnati ta shimfida

- Gwamnatin Kaduna ta bada umurnin rufe makarantu sakamakon waiwayen Korona ta biyu

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan otel ɗin da aka yi shirya gudanar da taron banbadewa zindir farkon makon nan a unguwar Barnawa dake jihar.

Hukumar cigabar cikin garin Kaduna KASUPDA ta bayyana cewa an rusa gidan badalar ne bayan gudanar da bincike kan wajen.

KASUPDA ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook inda ta daura hotunan yadda aka ruwa wajen.

A cewar KASUPDA, mammalakan dakin Otal din mai suna Asher dake Unguwar Barnawa sun saba dokokin hana yaduwar cutar Korona da gwamnatin jihar ta gindaya duk da gargadi da barazanar da gwamnan jihar yayi.

Hakazalika otal din aka shirya wannan taron banbadewa tsirara da aka shirya a jihar.

Hukumar tace: "KASUPDA ta rusa Asher Hotel dake Barnawa, karamar hukumar Kaduna ta kudu."

"Asher Hotel ya kasance wurin da aka shirya taron holewa zindir. Hakazalika an damke gidan da saba dokar hana yaduwar COVID-19 da hukumar ta shimfida."

Kalli hotunan:

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)
Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna) Hoto: KASUPDA
Source: Facebook

KU KARANTA: Kowa ya saurara, Buhari zai yi jawabi ga Najeriya da safiyar Juma'a: Garba Shehu

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)
Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna) Hoto: KASUPDA
Source: Facebook

KU DUBA: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 (Hotuna) 3

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)
Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna) Hoto: KASUPDA
Source: Facebook

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna)
Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan aka shirya banbadewa zindir (Hotuna) Hoto: Abdul
Source: Twitter

A wani labarin kuwa, hukumar yan sandan Najeriya ta ki sakin Mulhidi, Mubarak Bala, duk da umurnin da babban kotun tarayya tayi cewa Sifeto Janar na yan sanda ya sake shi.

An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Afrilu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

A ranar 21 ga Disamba, 2020, kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala cikin gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel