Kowa ya saurara, Buhari zai yi jawabi ga Najeriya da safiyar Juma'a: Garba Shehu

Kowa ya saurara, Buhari zai yi jawabi ga Najeriya da safiyar Juma'a: Garba Shehu

Kamar yadda ya saba, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabin sabon shekara ga yan Najeriya gobe Juma'a, 1 ga watan Junairu, 2021 misalin karfe 7 na safe.

Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Alhamis a shafinsa na Tuwita.

Garba Shehu ya yi kira da gidajen talabijin, rediyo da jaridun yanar gizo su garzaya tashar NTA da FRCN domin haska jawabin.

"Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin sabon shekara ga kasa ranar Juma'a. 1 ga Junairu, 2021 misalin karfe 7," Garba Shehu ya bayyana.

Kowa ya saurara, Buhari zai yi jawabi ga Najeriya da safiyar Juma'a: Garba Shehu
Kowa ya saurara, Buhari zai yi jawabi ga Najeriya da safiyar Juma'a: Garba Shehu Hoto: NGRPresident
Source: Twitter

Source: Legit

Online view pixel