Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 (Hotuna)

- Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin N13.588 tiriliyan na 2021

- Yau Alhamis ne ranar karshen shekarar 2020

Labari da duminsa na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021, mako guda bayan majalisar dokokin tarayya ta mayar masa da shi.

Buhari ya sanya hannu ne a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, birnin tarayya Abuja.

Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita da safiyar Alhamis, 31 ga Disamba, 2020.

Wadanda suka halarci taron sune; mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai. Femi Gbajabiamila; shugabannin majalisa, da kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa da na wakilai.

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 Credit: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Duk da umurnin kotu, an ki sakin Mubarak Bala daga gidan yari

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Asali: Facebook

KU KARANTA: Manyan ayyuka 9 da ma'aikatar Pantami ta gudanar a shekarar 2020

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Asali: Facebook

Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Yanzu-yanzu: Buhari ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021
Asali: Facebook

Mun kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari yau, Alhamis, 31 ga Disamba, 2020, zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 da majalisar dokokin ta amince da shi makon da ya gabata.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya tabbatar da hakan.

A ranar Litinin, fadar shugaban kasa ta karbi daftarin kasafin kudin daga wajen yan majalisa.

A ka'ida idan yan majalisar dokoki suka amince da kasafin kudin kuma suka kai fadar shugaban kasa, za'a gayyaci ministoci su duba.

Manufar haka shine tabbatar da cewa irin sauye-sauyen da yan majalisan suka yiwa kasafin kudin.

A ranar 21 ga wata, majalisar dattawa Najeriya ta amince da kasafin kudin N13.588 tiriliyan na shekarar 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar watanni biyu baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel