Duk da umurnin kotu, an ki sakin Mubarak Bala daga gidan yari

Duk da umurnin kotu, an ki sakin Mubarak Bala daga gidan yari

- Kotu ta bada umurnin sakin, Mubarak Bala, mutumin da ake zargi da yi wa Annabi Muhammad batanci a Facebook

- Yan sanda sun kama Mubarak Bala ne a Kaduna daga bisani aka kai shi Kano inda aka cigaba da tsare shi

- Kotun ta yanke cewa an keta hakokinsa na dan adam saboda tsare shi tsawon lokaci ba tare da bashi damar ganin lauyoyinsa ba kuma ta umurci a biya shi N250,000

Hukumar yan sandan Najeriya ta ki sakin Mulhidi, Mubarak Bala, duk da umurnin da babban kotun tarayya tayi cewa Sifeto Janar na yan sanda ya sake shi.

An kama, Bala, shugaban Humanist Association of Nigeria, a watan Afrilu a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sun shigar da kara a kansa inda suke zargin ya yi wa Annabi Muhammad batanci a shafinsa na Facebook.

A ranar 21 ga Disamba, 2020, kotu ta bada umurnin sakin Mubarak Bala cikin gaggawa.

Amma an samu labarin cewa har yanzu ba'a saki Mubarak ba kuma a Kurkuku ya kwashe hutun Kirismeti kuma a ciki zai yi hutun sabuwar shekara idan ba'a sakeshi yau Alhamis ba.

Yayin tattaunawa da PUNCH ranar Talata, lauyan Mubarak, James Ibor, ya ce hukumar yan sanda ba tada niyyar bin umurnin kotun.

Ibor yace: "Kotu ta bada umurni kuma an mikawa yan sanda amma sun ki bi."

"Mun aike wasika ofishin yan sanda, mun yi kiraye-kiraye, wasu ofisohin jakadanci sun sa baki. Mun tabbatar da cewa an kai musu umurnin saboda basu zo kotu ba."

"Basu daukaka kara ba. Kuma ba shari'ar da zasu iya daukaka kara bane. Wannan hukuncin karshe ne saboda kotu ta basu dama sosai."

"Kullum ana dage zaman saboda su, basu shigar da komai ba, kawai daina zuwa kotu sukayi."

KU KARANTA: Rashin tsaro: Wannan gwamnatin ta gaji matsaloli ne daga wacce ta wuce, Jigon APC

Duk da umurnin kotu, an ki sakin Mubarak Bala daga gidan yari
Duk da umurnin kotu, an ki sakin Mubarak Bala daga gidan yari Hoto: Facebook/Mubarak Bala
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari zai rattafa hannu kan kasafin kudin 2021 yau

A ranar 21 ga Disamba, Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umurnin sakin Mubarak Bala.

Da ya ke yanke hukunci kan karar da lauyoyin Bala suka shigar na zargin keta hakkinsa na bil adama, Mai shari'a Inyang Ekwo ya ce tsare Bala da 'yan sanda suka yi na tsawon watanni ya keta hakkinsa na 'yanci, adalci, zirga-zirga da 'yancin tofa albarkacin bakinsa.

"Rashin barin wanda ake zargi ya gana da lauyoyinsa keta hakkinsa na adalcin shari'a ne da samun lauya kamar yadda ya ke a karkashin sashi na 34 da 35(2) a karkashin kudin tsarin kasa ta 1999." yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel