'Yan sanda sun kama wadanda ke shirin yin chasu na badala a Kaduna

'Yan sanda sun kama wadanda ke shirin yin chasu na badala a Kaduna

- Rundunar 'yan sanda a Jihar Kaduna ta kama wadanda suke shirin yin chasu na badala a Jihar a ranar 27 ga watan Disamba

- Sanarwar shirin yin chasun da aka ce mahallarta za su tafi wurin babu tufafi a jikinsu ya tada hankulan gwamnatin Kaduna

- Hakan yasa gwamnan Jihar ya bada umurin bincike tare da kama wadanda ke shirin yin chasun na badala

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wadanda suke shirya taron chasu na badala karo na farko a Jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Sai dai an soke yin biikin da ake shirya yi a ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2020 duk da cewa ya yi suna a dandalin sada zumunta.

Daya daga cikin ka'idojin da masu shirya bikin suka saka shine mutane za su iso wurin ba tare da tufafi ba duk da cewa maza da mata ne za su hallarci chasun.

Yan sanda sun kama wadanda ke shirin yin bikin badala a Kaduna
Yan sanda sun kama wadanda ke shirin yin bikin badala a Kaduna. Hoto: @Channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

Bikin da ake shirin za a fara daga dare har safe an ce wadanda za su hallarta za su biya kudin da ya kama daga naira 2000 zuwa naira 3000 ko 5000 ga wadanda za su shiga sashin muhimman mutane.

Sai dai, gwamnatin Jihar ta yi gaggawan soke bikin tare da bada umurnin a kama wadanda suka shirya bikin.

Mataimaki na musamman ga Gwamna Nasir El-Rufai kan kafafen watsa labarai, Abdullah Yunus, ya ce yan sanda sun shiga cikin batun kuma an kama wasu.

Ya ce yan sanda sun dauki mataki cikin gaggawa saboda tallar da suka gani an wallafa a shafukan sada zumunta.

KU KARANTA: Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

"Da muka gano abinda ake shirya wa, gwamnati ta damu, don haka, Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da 'yan sanda," in ji shi.

Kakakin 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, a ranar Laraba, ya tabbatar da cewa jami'ansu sun gano inda ake shirin yin bikin sun kama wasu.

Sai dai ba bayyana adadin mutanen da aka kama ba inda ya ce idan sun kammala bincike za su yi fitar da sanarwa.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel