Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin shanu saboda yaki siyan shanun sata

Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin shanu saboda yaki siyan shanun sata

- 'Yan bindiga sun hallaka wani mashahurin dillalin shanu a karamar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara saboda yaki siyan shanun sata

- Wata majiya ta bayyana cewa sun dade suna kawo masa shanun satar sai dai ya shaida musu cewa ya daina harkar saboda yanayin yadda kasuwanni suka cika da shanun sata

- Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin hukumar yan sandan Jihar Zamfara ba game da lamarin

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun mamaye kauyen Sabon Garin Tafkin Kazai a karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara tare da kashe wani sanannen mai siye da siyar da shanu saboda yaki siyan shanun da suka sato, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun shaidawa wakilinmu cewa yan bindigar sun mamaye yankin kuma suka tafi kai tsaye wajen mai siyar da shanun, Alhaji Audu Mai sayen Shanu, wanda aka fi sani da Audu na Yar yaye, suka harbe shi kusa da kusa suka kuma tsere.

Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dilalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata
Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dilalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An yanke wa ƴan ta'adda 168 hukuncin ɗaurin rai-da-rai - Rahoto

"Alhaji Audu ya shahara a gabashin karamar hukumar Tsafe.

"A takaice, zai iya zama wanda yafi kowa shahara a harkar siye da siyar da shanu a yankin.

"Yan bindigar tun da farko sun mamaye kauyen tare da kwashe duka dabbobin da ke yankin kusan sau uku.

"Sun sha kawo masa irin dabbobin da suke satowa sai dai yaki amincewa da bukatar siyan su.

"Ya fada musu cewa ya daina harkar shanu tun lokacin da ya fuskanci shanun sata sun cika kasuwanni a yan shekarunnan.

KU KARANTA: An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina

"Bayan sun kashe shi, sun gudu ba tare da daukar ko tsinke daga gare shi ba.

"Da yawa daga makwabtan yankin ba su san an kashe shi ba sai daga baya saboda shi kadai aka kawowa hari," wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust.

Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

A wani rahoton, gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karyata jita jitar da ke cewa ya tafi Amurka ne don duba lafiyarsa, ya kuma bayyana cewa yaje Amurka don ziyartar yayan sa yayin da ya ke hutun karshen shekara.

Gwamnan ya yi ikirarin ne lokacin da ya bayyana a hirar gidan talabijin na Channels, kamar yadda kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sule, wanda ake ganin ya wofantar da asibitocin jihar don tafiya duba lafiya zuwa Amurka, ya bayyana cewa yana daukar hutun shekara a watan Disamba kuma yayi amfani da wannan damar don ziyartar iyalan sa a Houston, Texas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel