Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook

- Kotu a Jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum hukuncin zaman gidan yari saboda ɓata wa Gwamna Badaru suna

- Sabi'u Ibrahim Chamo ya yi ikirarin cewa Gwamna Badaru ya karbi kudin wasu yan APC da sunan zai basu tikitin takara

- Da aka gurfanar da shi a kotu, wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce bashi hujja kan iƙirarin da ya yi

Alƙalin kotun majistare da ke zamanta a Jigawa ta yanke wa wani Sabi'u Ibrahim Chamo hukuncin gidan yari saboda ɓata sunan Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar.

An fara kama Mista Chamo ne a jajiberin ranar Kirsimeti sannan aka tsare shi kafin gurfanar da shi a gaban kotu bayan ya kasa bada hujja kan zargin da ya yi a Facebook, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru kazafi a Facebook
Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru kazafi a Facebook. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

KU KARANTA: An yanke wa ƴan ta'adda 168 hukuncin ɗaurin rai-da-rai - Rahoto

Mutumin da aka yanke wa hukuncin ya yi zargin cewa gwamnan ya yaudari masu neman takara da yawa a APC ta hanyar karbar kudinsu da nufin basu tikitin takara.

Yayin shari'ar, bayan karanto masa abinda ake zarginsa da aikatawa, Mista Chamo ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Daga nan, kotu ya yanke masa hukuncin watanni shida a gidan yari da zabin biyan tarar N20,000 da bulala 20 a matsayin izina ga sauran al'umma.

A watan Yunin 2017, an tsare wani mai sukar gwamnan, Zakari Kafin Hausa, na tsawon kwanaki saboda sukar gwamnan a dandalin sada zumunta.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164