An maka matashi a kotu bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo a kirji

An maka matashi a kotu bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo a kirji

- Matashi mai shekaru 25 ya gurfana a gaban kotu bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo a kirji

- Kamar yadda dan sanda mai gabatar da karar ya sanar, ya aikata laifin a ranar 25 ga Disamba

- Ya tabbatar da cewa lamarin ya azabtar da budurwar domin kuwa har fasa mata kirji yayi

An maka wani matashi mai shekaru 25 mai suna Chibuike Njokwu a gaban kotun majistare da ke Ado-Ekiti a ranar Laraba bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo a nononta na hagu.

'Yan sanda sun zargi Njokwu da ke zama a yankin Surulere kusa da titin Basiri da ke Ado-Ekiti da cin zarafi tare da azabtar da budurwar.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Oriyimi Akinwale, ya sanar da kotun cewa wanda ke kare kansa ya aikata laifin a ranar 24 ga watan Disamba wurin karfe 7 na safe a Ado-Ekiti.

KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya waske, ya ki bayyana inda uwargidan shugaban kasa take

An maka matashi a kotu bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo
An maka matashi a kotu bayan ya gantsarawa budurwarsa cizo. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Akinwale ya zargi wanda ake karar da cizon budurwar mai suna Ifunanya Okonkwo a nononta na hagu inda ya fasa mata shi.

Ya ce wanda ake karar ya kasance saurayin budurwar kuma ya kai mata wannan harin ne yayin da suka samu dan hargitsi.

Laifin ya ci karo da tanadin sashi na 335 na dokokin manyan laifuka na jihar Ekiti na 2012.

Dan sanda mai gabatar da karar ya bukaci kotun da ta dage sauraron shari'ar zuwa lokacin da za su tattaro shaidu.

Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, Daily Trust ta wallafa.

Lauyan wanda ake zargin, Emmanuel Sumonu, ya bukaci kotun da ta bada belin wanda yake karewa, lamarin da alkalin ta amince.

Ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 26 ga watan Janairun 2021 don cigaba da shari'ar.

KU KARANTA: Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci

A wani labari na daban, wata kotun kasar Saudi Arabia a ranar Litinin ta yanke wa wata Loujain al-Hathloul, daya daga cikin fitattun mata masu rajin kare hakkin mata shekaru biyar da wata takwas a gidan yari.

Kamar yadda rahotanni daga The Washington Post suka bayyana, 'yar gwagwarmayar an yanke mata hukunci ne a kan wasu laifuka da ke da alaka da ta'addanci, takarda daga 'yan uwanta ta tabbatar.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce zargin da ake yi mata duk a kan Hathloul na gwagwarmaya ne. Bukatar ta kawo karshen mulkin mallaka da maza ke yi a kan mata a kasar ne ya ja mata hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel