Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci

Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci

- Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamanin Twitter, Ngozi ta bada labarin yadda ango ya fusata a kan danginsa basu samu abinci ba

- Hakan ya kawo hargitsi tsakanin ango da amarya har amarya tace ta fasa auren duk da kuwa liyafar bikinsu ce

- Angon babu kakkautawa shima yace ya fasa auren, lamarin da ya tarwatsa auren baki daya kowa ya kama gabansa

Wata ma'abociyar amfani da kafar sada zumuntar zamani mai suna Ngozi ta bar mutane da abun mamaki a labarin da ta bada.

A wasu jerin wallafar da tayi, Ngozi ta bada labarin yadda rikici ya barke bayan ango ya harzuka kan cewa danginsa basu samu abincin biki ba.

Amarya ta fusata bayan angon ya yi mata ihu tare da tsawa a gaban kowa. Ta je bashi hakuri tare da yi masa bayani amma sai ya fusata ya yi mata tsawa a gaban kowa.

Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci
Auren soyayya ya tarwatse a wurin liyafa saboda dangin amarya sun hana na ango abinci. Hoto daga Rubberball/Mike Kemp
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Zakzaky da wasu fitattun mutum 3 da suka yi Kirsimeti a gidan yari

Ngozi ta bada labarin yadda amaryar ta yi shiru tare da komawa mazauninta.

Amma kuma lokacin tafiya yana yi amarya tace wa ango ta fasa auren. A maimakon yayi kokarin gyarawa, sai yace shima ya fasa auren.

Ngozi ta wallafa: "A karshe dai amarya da dangin ango sun samu rikici. Kowa ya kama gabansa har da ango da amarya."

KU KARANTA: Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti

Wallafar da tuni ta karade kafafen sada zumuntar zamani ta janyo cece-kuce daga jama'a.

Wasu sun Dora wa amarya laifi yayin da wasu suka ga laifin ango. Wasu kuwa cewa suka yi ango ya birgesu da bai tsaya wani ja-in-ja ba, shima yace ya fasa.

A wani labari na daban, a halin yanzu, majalisar wakilai bata da bukatar ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa a kan matsalar tsaro da ya addabi fadin kasar nan, jaridar The Nation ta tabbatar da hakan a ranar Asabar.

Shugaban majalisar kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, ya gano cewa gayyatar farko ta koma ta kabilanci da siyasa.

An gano cewa wasu 'yan majalisar da suka assasa gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bai wa fadar shugaban kasan hakuri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel