Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar
- Kotun kasar Saudi Arabia ta yanke wa wata matashiya 'yar gwagwarmaya hukuncin shekaru biyar a gidan yari
- Matashiya Loujain al-Hathloul mai shekaru 31 a duniya ta sha gwagwarmaya har aka bar mata fara tuki a kasar
- An damketa a shekarar 2018 inda aka garkameta sannan kasar Saudi Arabia ta baiwa mata damar tuki
Wata kotun kasar Saudi Arabia a ranar Litinin ta yanke wa wata Loujain al-Hathloul, daya daga cikin fitattun mata masu rajin kare hakkin mata shekaru biyar da wata takwas a gidan yari.
Kamar yadda rahotanni daga The Washington Post suka bayyana, 'yar gwagwarmayar an yanke mata hukunci ne a kan wasu laifuka da ke da alaka da ta'addanci, takarda daga 'yan uwanta ta tabbatar.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce zargin da ake yi mata duk a kan Hathloul na gwagwarmaya ne. Bukatar ta kawo karshen mulkin mallaka da maza ke yi a kan mata a kasar ne ya ja mata hakan.
KU KARANTA: Da duminsa: A lokaci daya 'yan Boko Haram suna kai hari a kauyuka 3 na Borno
Kotun ta dakatar da wani bangare na hukuncinta, wanda ke nuna cewa akwai yuwuwar a sako Hathloul cikin watanni kadan.
Hathloul mai shekaru 31 an san ta da gangami a kan kare hakkin mata har ta kai ga fafutukar neman musu 'yancin tuka mota a kasar.
An tsareta tun a watan Mayun 2018 a wani kama mata masu rajin kare hakkin mata da gwamnatin kasar ta yi.
Bayan kwanaki da damketa, gwamnatin kasar Saudi ta bai wa mata damar tuka mota a kasar.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Majalisa ta janye gayyatar Buhari, ta bai wa fadar shugaban kasa hakuri
A wani labari na daban, daruruwan mazauna kauyukan Shindifu, Kirbutu, Debiro, Shafffa, Tashan Alade da Azare a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno sun fara komawa gidajensu don ganin barnar da 'yan Boko Haram suka yi musu a yammacin Asabar.
Mayakan ta'addancin sun kai hari a lokaci daya yankunan kasa da sa'o'i 48 da suka kai hari garin Garkida da ke jihar Adamawa, Vanguard ta wallafa.
Da yawan mazauna karamar hukumar Hawul Kirisitoci ne kuma tana da nisan a kalla kilomita 200 daga Maiduguri.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng