Hadimin Aisha Buhari ya waske, ya ki bayyana inda uwargidan shugaban kasa take
- Mai magana da yawun uwargidan shugaban kasa Buhari, Aliyu Abdullahi ya ki bayyana takamaiman inda uwar dakinsa take
- Abdullahi ya ce uwardakinsa tana da dama tare da hakkin sirranta lamurran rayuwarta duk da kuwa 'yar Najeriya ce
- Ya sanar da hakan ne yayin da aka tambaye shi inda uwargidan shugaban kasan take da ba a ganinta cikin jama'a
Aliyu Abdullahi, mai magana da yawun Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce tana da damar sirranta lamurranta.
Abdullahi ya sanar da hakan ne yayin martani a kan inda uwargidan shugaban kasan take da ba a ganin ta a kwanakin nan cikin mutane.
Ya sanar da hakan a ranar Talata a shirin siyasarmu a yau da gidan talabijin na Channels ya shirya, jaridar The Punch ta kiyaye.
KU KARANTA: Daruruwan mazauna kauyukan Borno sun koma gida baya gigita su da Boko Haram tayi a jajiberin Kirsimeti
A yayin da aka tambayesa inda uwargidan shugaban kasan take, hadiminta yace, "Duk da uwargidan shugaban kasan 'yar Najeriya ce, tana da damar sirrinta lamurranta. Wannan hakkinta ne kuma idan bata son fitowa ko magana ga jama'a ba wani abu bane."
Abdullahi ya kara da cewa akwai banbanci tsakanin salon yakar rashin tsaron Buhari a kasar nan da na tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ya ce, "Ka je arewa maso gabas, ni kaina daga can nake. Kafin zuwan Buhari, da yawanmu ba mu iya ziyartar garuruwanmu. A koda yaushe bama-bamai ke tashi amma yanzu ba hakan bane.
"Toh kuwa idan ba za mu godewa gwamnatin nan ba a kan kokarin da tayi a yankinmu, ta ina za mu iya gode mata a fannin tattalin arziki da ababen more rayuwa."
KU KARANTA: Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar
A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda Janar Olu Bajowa mai ritaya ya ceci rayuwarsa inda ya tsallake mutuwa daga hannun Buka Suka Dimka a juyin mulkin 1976.
Obasanjo ya ce da Bajowa bai gayyacesa sunan dan sa ba, da tuni sojoji masu juyin mulki sun hallaka shi har lahira.
Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020 a jihar Ondo yayin bikin murnar cikar Bajowa shekaru 80 a duniya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng