Lassa Fever: Mutum 242 sun mutu daga cutar a 2020, NCDC

Lassa Fever: Mutum 242 sun mutu daga cutar a 2020, NCDC

-Mutum 242 suka mutu daga cutar Zazzabin Lassa a shekarar 2020

-Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria ce ta fitar da hakan

-Cutar ta samo asali ne a wani gari a arewacin Nigeria inda aka fara gano ta

Akalla mutum 242 ne suka rasa rayaukansu sanadiyyar cutar Zazzabin Lassa a shekarar nan a Nigeria.

Hakan na kunshe ne a wani rahoto da cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria ta saki kamar yadda The punch ta ruwaito.

Zazzabin Lassa cuta ce da take yaduwa a cikin mutane ta abinci ko kayan amfanin gida da kashin Bera ko fitsarinshi ya taba.

KU KARANTA: Sojojin Nigeria uku sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno

Lassa Fever- Mutum 242 suka mutu daga cutar a 2020, NCDC
Lassa Fever- Mutum 242 suka mutu daga cutar a 2020, NCDC
Asali: UGC

Cutar ta bazu a kasashen Afrika na yamma, kuma an samo asalin sunanta daga wani gari mai suna Lassa a arewacin Nigeria inda aka gano cutar a karon farko a shekarar 1969.

KU KARANTA: An Kashe yan bindiga 6 a Borno

Kasashen da ta bazu sune- Sierra Leone, Liberia,Guinea da Nigeria. Sannan sauran kasashen dake makwabtaka dasu suna cikin hatsarinta.

Game da rahoton NCDC, Mutum 1175 ne suka kamu da cutar a Nigeria a shekarar 2020, sannan 817 ne suka kamu a shekarar 2019.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:https://facebook.com/legitnghausa

https://www.youtube.com/watch?v=qTZdAG8fJ6s&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel