Sojojin Najeriya 3 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno

Sojojin Najeriya 3 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno

- Sojojin Najeriya uku sun rasu sakamakon fashewar nakiya da Boko Haram suka birne a titi

- Sojojin na kan hanyarsu zuwa Gomboru Ngala ne don yi wa wasu matafiya rakiya

- Nakiyar da sojojin suka taka ya yi sanadin lalacewar motarsu tare da jikkata wasu da dama

A ƙalla sojoji uku ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu suka jikkata a lokacin da tawagar sojin suka taka wata nakiya da ƴan Boko Haram suka birne a hanyar Maiduguri/Gomboru Ngala a ranar Litinin, a cewar majiyoyi.

Daily Trust ta ruwaito cewa tawagar bataliya ta uku ta rundunar sojin Najeriya tana yi wa matafiya rakiya ne a lokacin da ta taka nakiyar a tsakanin Gomboru Ngala da Dikwa.

Sojojin Najeriya 3 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno
Sojojin Najeriya 3 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

A cewar wani majiya, wadda ya nemi a sakayya sunansa, "Motar sojojin ya lalace kuma mun rasa wasu dakaru sakamakon nakiya da aka birne a hanyar Dikwa/Gomboru Ngala.

"Muna addu'a Allah ya gafarta musu tare da yi wa iyalensu kaje," in ji majiyar.

Kazalika, wani babban nahiyar tsaro ya tabbatar da "dakaru uku sun sadaukar da rayuwarsu", ya ƙara da cewa motarsu ta lalace.

"Abin baƙin ciki ne, mun rasa sojoji uku sakamakon nakiya da suka taka.

KU KARANTA: Dan majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo a matsayin jari (Hoto)

"Sun mutu a hanyarsu na zuwa Gamboru Ngala sakamakon nakiya da Boko Haram suka birne a bangaren titin a ranar Litinin," majiyar tsaron ya ce.

A lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar soji ba ta fitar da sanarwa game da afkuwar lamarin ba.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164