An yanke wa ƴan ta'adda 168 hukuncin ɗaurin rai-da-rai - Rahoto

An yanke wa ƴan ta'adda 168 hukuncin ɗaurin rai-da-rai - Rahoto

- Wata kotu da ke kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu 'yan ta'addan kungiyar Wilayat Sinai

- Hakan na zuwa ne bayan samunsu da laifuka daban-daban da suka hada da kai harin ta'addanci da alaka da kungiyar IS

- An kuma yanke wa wasu yan kungiyar ta Wilayat Sinai 36 hukuncin zaman gidan yari da ya kama daga shekaru 3 zuwa 10

Kotun sojoji a kasar Masar, a ranar Talata ta yanke wa 'yan ta'adda 168 hukuncin daurin rai da rai saboda alakarsu da kungiyar ta'addanci ta Wilayat Sinai da ta kai hare-haren ta'addanci 63 a Alkaryar Sinai kuma tana da alaka da kungiyar IS, jaridar Masry Al-Youm ta ruwaito.

An kuma yanke wa wasu yan kungiyar Sinai 36 hukuncin shekaru 15 a gidan yari, kamar yadda jaridar ta ruwaito, ta kara da cewa ana zargin wadanda aka yanke wa hukuncin da laifin kafa kungiyoyi 43 masu yi wa IS biyaya tare da aikata laifuka a arewacin alkaryar.

An yanke wa 'yan ta'adda 168 hukuncin daurin rai da rai - Rahoto
An yanke wa 'yan ta'adda 168 hukuncin daurin rai da rai - Rahoto. Hoto: ABC News
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina

Kotun ta kuma yanke wa wasu 'yan tada kayan baya 270 hukuncin gidan yari da ya kama daga shekaru 3 zuwa 10 sannan ta gurfanar da wasu mutum 35 da ake zargi, Vanguard ta ruwaito.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa an bawa mambobin kungiyoyin da dama horo a sansanin 'yan tada kayan baya da ke kasar Syria.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya 3 sun mutu bayan motarsu ta taka nakiya a Borno

Har wa yau, an gano 'yan ta'adda na sa ido kan ginin Ma'aikatar Harkokin Kasar Waje na Masar da makarantar horas da 'yan sanda na kasar da ke New Cairo da jiragen ruwan da ke bi ta Suez Canal da coci-coci da dama da niyyar kai musu harrin ta'addanci.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164