An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina

An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina

- An ceto mutane 23 da suka hada da kananan yara da mata wanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a wata musayar wuta a Jihar Katsina

- Yan bindiga shida aka kashe yayin musayar wutar tare da gano dabbobin da suka sace da kuma babura harma da bindiga

- Kakakin yam sandan jihar ya bayyana cewa sun yi wa yan bindigar kawanya bayan sun sami labarin gaggawa na harin da suka kai kauyen Lambo a Kurfi

An kashe yan bindiga da ba su gaza shida ba a wata musayar wuta tsakanin su da jami'an tsaro ranar Talata a karamar hukumar Kurfi da ke jihar Katsina, Vanguard ta ruwaito.

An ruwaito cewa mutane 23 da suka hada da mata da kananan yara wanda yan bindigar suka yi garkuwa dasu lokacin da suka kai hari kauyen Lambo a karamar hukumar Kurfi suma an ceto su yayin barin wutar.

An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina
An kashe 'yan bindiga 6 a Katsina. Hoto: @channelstv
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hattara: Hanyoyi 4 da zaka iya kare kanka daga masu 'sace' bayanan katin ATM ɗin ka

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yan bindiga da suka haura 30, suna harbe harbe a iska da bindigun AK 47, suka kai hari kauyen tare da kashe mutane biyu da yin garkuwa da mutane 23 (mata 17 da kananan yara 6).

SP Isah ya ce samun labarin jami'an tsaro ke da wuya suka shiga fafutuka tare da yiwa yan bindigar kawanya wanda ya yi sanadiyar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da dabbobin da aka sace.

A cewar sa, "da misalin karfe 2:30 na ranar Talata, yan bindiga da yawan su ya haura mutane 30, suna harbe harbe a iska, suka kai hari kauyen Lambo, mazabar Wurma, karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, sun kashe mutum biyu tare da garkuwa da mata 17 da kananan yara 6.

"Jami'an yan sanda, sojojin sama da na kasa duk sun samu masaniya kuma sun toshe duk wata hanya da zasu iya guduwa.

KU KARANTA: Ba likitoci na tafi gani ba, hutu na tafi don in ga yara na, Gwamna Sule

"Haka zalika, jami'an sun yi yan bindigar kawanya a tsakanin kauyen Ummadau zuwa Kwayawa kuma aka yi musayar wuta, lamarin da ya janyo mutuwar yan bindiga 6, ceto duka mutane 23 da akayi garkuwa da su, an gano shanu 23, tumaki 20, da kuma akuyoyi 31 tare da kwace babura 12 da bindiga guda daya kirar G3.

"Hukumomi na ci gaba da bincike don kama ragowar bata gari ko kuma gano gawarwaki.

"Ana ci gaba da bincike," SP Isah ya bayyana

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel