Yan Najeriya sun caccaki Bill Gates kan jawabin da yayi na rashin yawaitar Korona a Afrika

Yan Najeriya sun caccaki Bill Gates kan jawabin da yayi na rashin yawaitar Korona a Afrika

Yan Najeriya a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun caccaki mu'assasin kamfanin Microsoft Bill Gates, kan jawabin da yayi na cewa bai san dalilin da ya sa mutane da yawa basu kamu da Korona a Afrika kaman sauran kasashe.

Gates, a jawabin da aka saura a shafinsa, ya bayyana cewa da yiwuwan an yi karya kan adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Afrika.

Attajirin da matarsa, Melinda Gates, a baya sun yi kiyasin cewa nahiyar Afrika ce za ta fi fuskantar kalubale daga annobar COVID-19.

Amma wannan kiyasi da suka yi bai kasance gaskiya ba saboda Korona ba tayi wa nahiyar Afrika diban karan mahaukaciya kamar yadda sukayi tunani.

Mun kawo muku karshen mako cewa, Bill Gates, daya daga cikin shugabannin gidauniyar Bill da Melinda Gates (BMGF), ya ce har yanzu duniya ta kasa fahimtar dalilin da yasa masu korona a Afrika suka kasa yawa, The Cable ta wallafa.

Mai taimakon jama'an kuma dan Amurkan wanda yake saka hannayen jari a fannin lafiya ya ce, ya yi farin ciki da rashin hauhawar masu cutar a Afrika kamar yadda aka yi hasashe.

"Abu daya da nake farin ciki da rashin faruwar shine rashin tsanantar hauhawar cutar korona a kasashe masu tasowa," ya rubuta a jawabinsa na karshen shekara.

KU KARANTA: Yan bindiga na kokarin shigowa Najeriya daga kasar Mali ta jihata, Gwamnan Oyo

Yan Najeriya sun caccaki Bill Gates kan jawabin da yayi na rashin yawaitar Korona a Afrika
Yan Najeriya sun caccaki Bill Gates kan jawabin da yayi na rashin yawaitar Korona a Afrika Hoto: @NCDCgov
Source: Twitter

KU KARANTA: Duk Matafiyan Ingila da Afrika ta Kudu sai sun yi gwajin COVID-19 inji PTF

Musa Kaoje Umar yace: "Allah ya fika oga Mai daudar duniya Kuma duk wada kukeso Yan Africa su tagayyara idan Allah bai aminceba Babu wada zakuyi wallahi mugu Mai mugun nufi ta Allah ba taku ba....munga bayan tsarinku na polio da kanjamau haka Allah zai taimakemu muga bayan corona."

Adamu Jidagani yace: " ولا يحق المكر سيء إلا بأهله

KULLA MUNMUNAN MAKIRCI BAYA FADAWA SAI GA MESHI!!

Saboda haka in sha'Allahu akanku duk wani munmunan shiri da kukayi zai rinka karewa.

Tunda baku kuka halicci duniya ba, kuma halittaku akayi, kuma mai halittar yananan kuma yana tsare da kayansa,

Don haka in zakuyi imani dashi kuyi, domin shine mafita kawai."

Usman Isah Kebbe yace: "Dama sharri kuke nufi da nafiyar musulunci a siyasance kuna cewa taimakawa kukeyi.Yanzu ko kunfito fili karara kunnuna bakin cikinku Balai bai farmuna ba.To Allah keda LAFIYA da ciyo Ya Kare mu bawanda zai iya ABINDA Bai Yardaba.Allah MUN gode Ma."

Muhammad Ibrahim yace: "Allahu Akbar!! Rashin Sanin Allah da ciwo yake. Ai Allah Ne Ya Tsaremu daga mugun nufinku da mummunar manufarku akanmu. Ya Allah Muna qara GodeMa muna rokonKa Ka tsaremu daga dukkan abinda yafi qarfimu wadda mukafi qarfinsama Ya Allah Ka taimakamana akansa."

Samuel Danladi yace: "Tunda baiyi tasiri a africa ba fatana shine kar a sake munmunan shiri wanda ciwon zai addabi africa, domin daman akwai harsashen cewa ciwon zai iya dawowa daga watan 11zuwa12, muna rokon Allah yakare mu da rigakafin da za'a mana a hannun dama mai dauke da lambobin shaidan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel