Yan bindiga na kokarin shigowa Najeriya daga kasar Mali ta jihata, Gwamnan Oyo
- Bayan bude iyakokin Najeriya, yan bindiga na kokarin shigowa Najeriya, cewar gwamnan Oyo
- Najeriya na da iyaka da kasar Mali ta garin Saki na jihar Oyo
- Gwamnan jihar ya tabbatarwa al'ummarsa cewa yana iyakan kokarin don kare hakan
Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya ce yan bindiga daga kasar Mali na kokarin shigowa Najeriya ta iyakar dake jihar.
Makinde, yayi jawabi yayinda ya kai ziyara yankin Oke-Ogun dake jihar, ya bayyana cewa yan bindigan na kokarin shigowa daga Mali ta garin 'Saki' dake jihar Oyo.
Ya bayyana hakan ne a fadar Okere of Saki, Khalid Olabisi, da kuma sauran sarakunan gargajiyan yakin Oke Ogun, Premium Times ta ruwaito.
Amma, ya tabbatarwa sarakunan cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokari wajen tabbatar da cigaban jihar da al'ummarta.
"Ko shakka babu a wajen nan, akwai matsalar yan bindiga. Misali, yankin Saki na da iyaka da wata kasa kuma wannan matsala ne saboda yan bindiga daga Mali na kokarin shigowa," yace.
"Muddin suka samu damar shiga waje suna kai hare-hare, ba zasu fita ba."
KU DUBA: Pantami ya umurci kamfanonin sadarwa su daina cire N20 don duba lamban katin zama dan kasa NIN
KU KARANTA: Kimanin ma'aikatan lafiya 500 suka kamu da cutar Korona a Abuja, FCTA
A bangare guda, Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya bukaci matasan Arewa su dena sukar Limamin cocin darikar Katolika na Sokoto, Mathew Kukah, a maimakon hakan su mayar da hankali wurin yakar 'yan bindiga da suka addabi yankin.
A sakonsa na Kirsimeti, Kukah ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da nuna son kai. Kukah ya ce Buhari ya sadaukar da burin da Najeriya ke niyyar cimma saboda son kai da fifita yankin Arewa a kan saura.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng