Duk Matafiyan Ingila da Afrika ta Kudu sai sun yi gwajin COVID-19 inji PTF
-Gwamnatin Tarayya ta kafa wasu sababbin dokokin yaki da Coronavirus
-PTF sun wajabtawa mutanen Ingila da Afrika ta Kudu gwajin COVID-19
-Sai an tabbatar da lafiyar duk wanda zai shigo Najeriya daga kasashen nan
Kamar yadda ake sa rai, gwamnatin tarayya ta kawo wasu sababbin matakai da za a bi domin takaita yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya.
Kamar yadda sanarwar da aka fitar ta bayyana, gwamnatin Najeriya za ta fara dabbaka wadannan matakai daga ranar 29 ga watan Disamba.
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yakar COVID-19, PTF, ya fitar da sanarwar a dazu.
Daga yau ranar Talata, an wajabtawa duk mutumin da ya shigo Najeriya daga kasar Birtaniya ko Afrika ta kudu yin gwajin kwayar Coronavirus.
KU KARANTA: Ma'aikatan lafiya 500 sun kamu da Coronavirus a Abuja
PTF ya ce sai an tabbatar duk wanda zai shigo Najeriya daga wadannan kasashe bai dauke da cutar COVID-19 da yanzu ta sake barkowa a Duniya.
Ga kadan daga cikin abin da sanarwar ta ke cewa:
“Kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar #COVID-19 ya shigo da matakai na musamman ga matafiyan kasar Birtaniya da kuma Afrika ta kudu.”
“Matafiyan da su ka fito daga wadannan kasashe biyu sai sun yi gwajin kwayar #COVID19 na PCR, sa’o’i 96 da shigowarsu Najeriya.” Inji kwamitin PTF.
KU KARANTA: Mai dakin El-Rufai ta ci gyaran turancin Atiku Abubakar
Jawabin ya ce: “Sannan sai sun gabatar da takardun biyan kudin sake yin gwajin COVID-19 a Najeriya.”
Dazu kun ji yadda alkaluman cutar COVID-19 su ka karyata duk abubuwan da gwamna Yahaya Bello yake fada game da yaduwar Coronavirus a Kogi.
Yahaya Bello ya na ta ikirarin babu wanda ya kamu da Coronavirus. Haka zalika gwamnan ya na da’awar cewa ana yi wa mutane gwajin cutar a jiharsa.
Alkaluman da su ka fito daga ma'aikatar NCDC ta kasa sun nuna mana ba haka abin yake ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng