Jami'in NSCDC da ya bindige mutum 2 har lahira ya ce 'iska' ya ke ƙoƙarin ɗumamawa

Jami'in NSCDC da ya bindige mutum 2 har lahira ya ce 'iska' ya ke ƙoƙarin ɗumamawa

- Jami'in hukumar Civil Defense Sunday Ada ya shaidawa yan sanda cewa ba niyya ya harbi matasa biyu da ake zargi ya harbe ba

- Ya ce yana kokarin harbin iska ne kuma bai ji lokacin da zasu wuce ba har ya harbi sama kuma tsautsayin ya afka musu

- An dai tsare shi ne bisa zargin sa da kashe matasa biyu yayin suke hanyar tafiya bikin Kirsimeti

Sunday Adakala Ada, wani jami'in hukumar tsaron Civil Defense wanda aka kama bisa zargin kashe wasu matasa biyu da ke tafiya bikin Kirsimeti a Otukpo ta Jihar Benue, ya bayyana yadda lamarin ya faru.

Jami'in tsaron wanda yan sanda ke tuhuma, ya ce yana kokarin harbin iska ne kuma bai ga tahowar kowa ba lokacin da ya harbi iska. Ya kara da cewa ba da gangan ya kashe su ba.

'Koƙarin ɗumama iska na ke yi: Jami'in NSCDC da ya bindige mutum biyu har lahira
'Koƙarin ɗumama iska na ke yi: Jami'in NSCDC da ya bindige mutum biyu har lahira. Hoto: @Lindaikeji
Asali: Instagram

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

Ada ya kara da cewa an shaida masa da farko cewa mutum daya ya mutu daya kuma ya ji rauni, amma mutane biyu ne suka rasu bayan ya yi harbin.

Kalli bidiyo a kasa;

KU KARANTA: Gobara ta cinye shaguna 252 a kasuwar Galadima

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel