Gobara ta cinye shaguna 252 a kasuwar Galadima
- Anyi gobarar da ta janyo asarar miliyoyin naira a kasuwar Galadima da ke Gwarimpa a birnin tarayya Abuja
- Masu shaguna da abin ya shafa sun bayyana irin asarar da suka tafka har ma wani tela yace basu san yadda za su biya mutane kayan su da suka kone ba
- Shugaban kasuwar ya jinjinawa hukumomin kashe gobara bisa namijin kokarin su wajen hana wutar haurawa makwabta
Shagunan da basu gaza 252 suka kone sanadiyar gobarar da ta afku kasuwar Galadima da ke Gwarimpa, Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Wata da abin ya shafa, Hajiya Falmata Bukar, wadda ta ke da gidan abinci da kuma kanti a cikin kasuwar, ta ce ta rasa komai nata sanadiyar wutar.
Ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 na rana, daidai lokacin da musulmi da kirista kowa ya tafi ibada, musulmi sallar juma'a su kuma kiristoci suna hotun Kirsimeti.
DUBA WANNAN: Katsina: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 48, sun kashe 2
"An fara gobarar ne bayan dawo da wutar lantarki. Ganin karfin wutar, ya saka na ce a kashe talabijin amma, cikin sakanni, wayar wuta ta kone kuma shagon ya kama da wuta" a cewar ta.
Regina Musa, wata mai shagon gyaran gashi, ita ma ta bayyana irin asarar da ta tafka, "nayi hada hada sosai daren da abin zai faru, saboda na samu kwastomomi da yawa, na shirya komawa shagon da sassafe, amma gajiya tasa na kasa fita.
"Wani makwabcin shagona, shi tela ne, ya kirani a waya ya shaida min wannan mummunan labarin. Na rasa komai; kayan aiki na kamar na'urar busar da gashi da ta dumama gashi, mayukan gashi da dama, generator da kuma kudi sanadiyar gobarar".
Shima wani tela, wanda abin ya shafa ya bayyana cewa ya rasa keken dinkin sa da kayyakin mutane wanda aka bashi aiki.
KU KARANTA: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle
"Da yawan teloli mun tafka asara ciki harda kayan mutane da ke shagon. Bamu san yadda zamu biya su ba," ya yi karin bayani.
Shugaban kasuwar, Sulaiman Musa, ya ce gobarar ta lalata kayayyakin miliyoyin naira, da ya ke yabawa jami'an kashe gobara bisa jajircewarsu.
Yace hukumomi uku daga hukumar kashe gobara ta birnin tarayya, NEMA da kuma sojojin sama, sun zo sun kuma yi namijin kokari wajen hana gobarar haurawa makwabta.
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.
Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.
Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng