'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

- Yan bindiga sun hallaka shugaban 'yan sintiti na garin Maigora da ke karamar hukumar Faskari a Katsina

- Mallam Ummaru Balli ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a Rimi

- Baya ga kashe shugaban 'yan sintirin, yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutane takwas da suka sace daga Rimi

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a daren Lahadi sun kashe shugaban kungiyar 'yan sintiri a garin Maigora a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, Malam Ummaru Balli.

Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum takwas yayin harin da suka kai a kauyen Rimi da ke karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutum 8 a Katsina
'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutum 8 a Katsina. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

An gano cewa Mallam Balli ya jagoranci wasu 'yan sintiri zuwa Rimi domin su taka wa 'yan bindigan da suka kai hari a Rimi birki a dare da abin ya faru kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mazauna garin sun bayyana cewa yan sintirin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan hakan ya yi sanadin rasuwar Mallam Balli.

Yan bindigan daga bisani sun tsere sun tafi daji da mutum takwas da suka yi garkuwa da su.

KU KARANTA: Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa

Tuni dai an yi wa Mallam Balli jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Kawo yanzu mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai riga ya yi tsokaci kan lamarin ba.

Kazalika, mai bawa gwamna Aminu Masari shawara kan tsaro, Mallam Ibrahim Katsina bai daga wayarsa ba kuma bai turo da amsar sakon kar ta kwana da aka aike masa ba a lokacin wallafa wannan labarin.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel