Korona ta hallaka tsohon gwamna a lokacin mulkin Babagangida

Korona ta hallaka tsohon gwamna a lokacin mulkin Babagangida

- Cutar korona ta hallaka tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soji, Air Commodore Idongesit Nkanga

- Kafin rasuwarsa, Nkanga shine shugaban kungiyar kishi da son cigaban yankin Neja-Delta (PANDEF)

- Marigayi Nkanga ya shugabanci jihar Akwa Ibom daga shekarar 1990 zuwa shekarar 1992 a lokacin mulkin Babangida

Annobar cutar korona ta zama sanadiyyar mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin mulkin soja, Air Commodor Idongesit Nkanga, a ranar Alhamis, kamar yadda NewswireNGR ta rawaito.

NewswireNGR ta rawaito cewa gidan talabijin na Channels ya wallafa cewa tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 68 a wani asibiti da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Ba'a bayyana sunan asibitin ba.

Marigayi Nkanga ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom daga watan Satumba na shekarar 1990 zuwa watan Janairu na shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Kafin rasuwarsa, marigayi Nkanga ya na rike da shugabancin kungiyar kishin yankin kudu maso kudu, Neja-Delta (PANDEF).

Korona ta hallaka tsohon gwamna a lokacin mulkin Babagangida
Korona ta hallaka tsohon gwamna a lokacin mulkin Babagangida @NewswireNGR
Source: Twitter

A matsayinsa na shugaban kungiyar PANDEF, Nkanga ya dade yana yakin neman sauya tsarin mulkin Nigeria da cigaban yankin Neja-Delta.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

A cikin wata hira da aka yi da shi a cikin watan Oktoba, Nkanga ya bayyana cewa ba zai taba daina kiran a sauya tsarin mulkin Nigeria ba.

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta rawaito cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.

Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel