Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su

- Daular Musulunci ta Usmaniyya ta kafu a shekarar 1299 sannan ta rushe a shekarar 1923

- Kafin rushewarta, Daular Usmaniyya, wacce ta yi shura a kasar Turkiyya, ta bayar da gudunmawa ga addinin Musulunci

- Babban malami, Sheikh Aminu Daurawa ya yi bayani a kan dalilin da yasa ake samun kayan tarihin annabi Muhammad a kasar Turkiyya

Daular Musulunci ta Usmaniyya (Othman Empire) ta wanzu tsawon kimamanin shekaru 600, tun bayan kafuwarta a watan Yulin shekarar 1299, kana ta wargaje a watan Oktoban shekarar 1923.

Daular ta samu sunanta daga sunan mutumin da ya kafata wato Usman, wanda ake kiransa da Attagul, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.

Shahararren malamin addinin Islama a arewacin Nigeria, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyanawa gidan labarai na BBC dalilin da yasa ake jingina Annabi da kayan tarihi da aka samu a Turkiyya.

KARANTA: Kotun ICC ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello, bayan ya samu kuri'u 5 cikin 110

"Hakan ya faru ne a lokacin Sarki Abdulhamid II a cikin shekarar 1914 lokacin da wani sarki ya yi yunƙurin kai farmakin ta'addanci garin Madina yayin yakin duniya na biyu, wanda hakan ne yasa Sarki Abdulhamid II yasa aka tara sojoji masu ɗumbin yawa tare da tura zuwa Madina don su bawa Musumi gudun mawa."

"Sannan kuma ya umarcesu su tattaro duk wasu kaya da suka danganci Annabi don kada a sake kwata irin ta Bagadaza, wato ƙona alkyabbar Annabi da 'yan ƙabilar Magul suka yi a wancan lokacin."

"Wannan yasa aka tattara duk wani kaya da ya danganci Annabi da aka samu.

"An kwashe su, an mayar da su Turkiyya don kare su daga sharrin maƙiya, da kuma basu kulawar da ta dace," a cewar Daurawa.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su @BBC
Asali: Twitter

Sawayen ƙafafun Annabi ne a jikin wannan dutsen da ke cikin hoton da ke sama. An nuna hoton a wani gidan adana kayan tarihi da ke Santambul, Turkiyya, tun ranar 16 ga watan Nuwamban 2017.

KARANTA: Kotun ICC za ta fara binciken hukumomin tsaron Nigeria, ta fadi dalili

Akwai ɗumbin kayan tarihi da ake samu a Santambul da ba kasafai ake samunsu daga sauran sassan duniyar da Musulunci ya mulka a baya ba.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Asali: Twitter

Hotunan Takubban Annabi kenan da wasu ƙwararrun maƙeran zinare a Daular Usmaniyya suka kerawa gidan adanawa.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su @BBC
Asali: Twitter

Hoton wata tasa kenan da aka yi amanna cewa Annabi ya yi amfani da ita wajen shan ruwa, kuma ta na ɗaya daga cikin kayyakin tarihin da aka yi holinsu a fadar Topkapi da ke birnin Santambul.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su @BBC
Asali: Twitter

Hajarul Aswad, wanda aka fi sani da 'Baƙin dutse', wani dutse ne mai tarihi da muhimmancin gaske. An nuna shi a baja kolin kayan tarihin kayan Musulunci a ranar 3 ga watan Yuli, 2018.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su @BBC
Asali: Twitter

Mazubar ruwan Ka'aba kenan, tana da muhimmanci da daraja a Musulunci. Ita ma an nuna ta a fadar Topkapi a ranar 3 ga watan Yuli, 2018.

Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su
Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su @BBC
Asali: Twitter

Wannan Shine silin gashin Annabi Muhammad da aka adana a cikin wani siririn bututu na musamman.

An nunawa ɗimbin masoya da mabiyan Annabi a duniya duk wadannan kayayyaki tare da wasu kayayyaki da ake dangantan su da shi.

A kwanakin baya ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugabar darikar Kadiriyya, Sheik Karibullah Nasiru Kabara, ya yi ikirarin cewa yana ajiye da silin gashin annabi da aka bashi kyauta.

Sheikh Karibu ya bayyana cewa wani balaraben kasar Daular Larabawa ne ya bashi kyautar zirin gashin wasu shekaru da suka gabata.

Sai dai, kalaman babban Malamain sun haifar da cece-kuce a tsakanin Musummai a dandalin sada zumunta.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel