Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

- Wani bidiyon hira da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da BBC Hausa ta wallafa ya haifar da cece-kuce

- A cikin faifan bidiyon, Sheikh Karibu ya yi tsokaci a kan rayuwarsa tare da yin waiwaye a kan rayuwarsa tun daga yarinta

- Babban malamin ya bayyana cewa har yanzu yana ajiye da zirin gashin manzon Allah (SWA) da aka bashi kyauta

Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, shugaban darikar Kadiriyya, ya yi ikirarin cewa har yanzu yana ajiye da zirin gashin manzon Allah (SWA) da aka bashi kyauta shekaru takwas ko tara da suka wuce.

Babban malamin ya bayyana faifan bidiyo hira da shi da sashen Hausa na BBC ya wallafa a shafinsa na tuwita.

Da ya ke amsa tambaya a kan wanne abun farinciki ne ya faru da ba zaka taɓa mantawa ba?

Sai Karibu ya ce; "akwai wani abu da wato idan na tuna shi nakanyi farinciki da gaske, na kan ji daɗi sosai shine wato wani mafarki dana taɓa yi tun ina ɗan ƙaramin yaro wataƙila ban fi shekara goma ba.

"Na yi mafarkin wato na taɓa samun wata wuƙa ta zinare, wani daga cikin manyan malaman mu ya bani ita a hannun dama, wani daga cikin manyan malaman ya sake bani wata wuƙar ta azurfa.

"Tun ina ƙaramin yaro, ina riƙe da mafarkin, na kasa mantawa da shi har sai Allah ya kawo wani lokaci ina jin zai kai kamar shekara takwas kenan ko tara, sai Allah ya kawo wani babban bawan Allah mutumin ƙasar Dubai (Abu-Dhabi) ana kiransa Alsheik Ahmadul Hazaraji, wannan bawan Allah, gidansu, wato gidane wanda ya ke ya yi fice tun tun tuntuni.

"Suna da gadon gashin Annabi (SAW), wato kakanninsa da kakannin kakanninsa, tun a wancan lokacin annabi (SAW) duk sanda ya yi aski ya kan ɗan rarrarabawa sahabbansa gashinsa, wani ya bashi da yawa, wani ya ba shi kaɗan, to sai ya zama yana rarraba musu, to shi kuma gashin yana da wata mu'ujiza ko wata kususiyya yadda ko shekara nawa zai yi baya canjawa, baya ruɓewa, baya lalacewa.

Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina najiye da zirin ganshi Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata
Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina najiye da zirin ganshi Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata @Kanofocus
Asali: Twitter

"Kwanaki na ji wani Program (Shiri) da ku ka yi, mutanen BBC suka yi a Turkiyya, irin wannan gashin an same shi da irin kayayyakinsa kusan shekara dubu da ɗari huɗu da wani abu, amma yana nan a irin yadda yake ba ya canjawa.

"Saboda wannan mafarki da nayi, Allah shi ya kawo wannan mutum, shi kuma yana da wannan gashin, suna da gadonsa, to sai ya ɗauko sili ɗaya irin wannan sai ya sako shi a wani gida wanda aka yi shi da gold (Zinare), ya kai tsawon hannuna haka, ɗayan kuma aka yi shi da azurfa fara, to sai ya sako wannan gashin ɗaya a cikin wannan, ɗaya a cikin wannan.

"A cikin filin taron Maulidi da maukibin da muke na Ƙadiriyya, ya zo ya bani kyautar wannan abun, ya bani shi, to wannan abu na kasa manta shi.

"Wannan wuƙar ta Zinare aka ban ita, na karɓa da hannun dama, da wuƙa ta azurfa da aka ban, ita ma na karɓa da hannun dama, sai gashi ashe wani hororo ne wanda aka yi shi kamar wata hasumiya, haka wanda aka sako gashin Annabi (SAW) a ciki, aka zo, aka bani kyautarsa, wannan abun ya bani mamaki ƙwarai."

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel