Majidadi, mahaifin tsohon gwamna Kwankwaso, ya rasu bayan gajeriyar jinya

Majidadi, mahaifin tsohon gwamna Kwankwaso, ya rasu bayan gajeriyar jinya

- Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa

- Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

- Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano

Majidadin masarautar Karaye kuma hakimin karamar hukumar Madobi, Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Marigayin shine mahaifi wurin tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya tabbatar mata da rasuwar basaraken sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

"Cikin juyayi da mika al'amuranmu ga Allah (SWT) muke sanar da rasuwar mahaifinmu Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, majidadin Kano/Makaman Karaye, wanda ya rasu yana da shekaru 93 a daren Juma'a, 25 ga watan Disamba, 2020, a Kano," kamar yadda Inuwa ya bayyana a cikin sanarwar.

Majidadi, mahaifin tsohon gwamna Kwankwaso, ya rasu bayan gajeriyar jinya
Majidadi, mahaifin tsohon gwamna Kwankwaso, ya rasu bayan gajeriyar jinya @Daily_nigerian
Asali: Twitter

Sanarwar ta cigaba da cewa; "marigayi Alhaji Musa Saleh Kwankwaso shine mahaifin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano. Ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya 19 (maza tara, mata 10) da jikoki da dama.

KARANTA: Bidiyon Sheikh Karibu Kabara: Ina ajiye da zirin gashin Annabi da aka bani kyauta shekaru 8 da suka gabata

"Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe 3:00 na ranar Juma'a, 25 ga watan Disamba, 2020, a Miller Road da ke cikin unguwar Bompai a birnin Kano.

"Dangi da iyalin marigayin na rokon masoya da magoya baya daga makwabtan jihohi da sauran wurare masu nisa cewa ba sai sun yi bulaguro zuwa Kano ba saboda dalilan tsaro. Mu na kira ga jama'a da su saka marigayin a cikin addu'a daga duk inda suke.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Injiniya Muneer Al-Jundi, mutumin da ya kera tare da jagorantar gina kofar dakin Ka'aba ta yanzu ya rasu.

Shekaru arba'in da uku kenan tun bayan da tsohon sarkin Saudia, Khalidi bin Andul Aziz, ya sauya kofar dakin Ka'aba.

Ya bayar da aikin kera sabuwar kofar ne ga kamfanin Injiniyarin na Sheikh Muhammad bin Badr a shekarar 1970.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng