Mutane sun tofa albarkacin bakinsu kan matashin da yayi ikirarin babu wanda ya isa ya kwace masa budurwa

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu kan matashin da yayi ikirarin babu wanda ya isa ya kwace masa budurwa

- Wani matashi mai suna, @sonofsamuel_ a shafin Tuwita ya ce babu wanda zai iya kwace masa budurwa

- Jawabin matashin ya sanya mutane tofa albarkatun bakinsu inda wasu ke masa dariya yayinda wasu ke masa addu'a

- Ba tare da bata lokaci, wani har ya cire hoton yarinyar domin nuna masa kwaceta ya fi komai sauki

Samuel, wani matashi ya bayyana a shafin Tuwita da sunan Ghana Kanye ya sanya mutane magana a sabon jawabin da ya daura.

A jawabin da Legit.ng ta gani, matashin ya daura hotonsa da na budurwarsa yana mai cewa, "babu mahalukin da zai iya kwace ki daga wajena, masoyiya."

Dubannan mutane sun tofa albarkacin bakinsu inda kowa ke bayyana ra'ayinsa.

Yayinda wasu ke kara masa karfin gwiwan ci gaba da soyayyarsa, wasu suna zaulayansa da cewa yana ruwa.

KU DUBA: An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu kan matashin da yayi ikirarin babu wanda ya isa ya kwace masa budurwa
Mutane sun tofa albarkacin bakinsu kan matashin da yayi ikirarin babu wanda ya isa ya kwace masa budurwa Hoto: @sonofsamuel
Source: Twitter

KU KARANTA: Cin zarafi da rashawa na yan sanda a Najeriya: Rahoto

A bangare guda, a kwanan ne wata kotu ta bukaci a binciki shahararren mawakin siyasan nan mazaunin Kano, Dauda Kahutu Rarara, bayan ikirarin cewa ya yi amfani da matar aure a daya daga cikin bidiyon da ya saki a kwanan nan.

A cewar rahotanni daga jaridar The Guardian, an yi zargin cewa Rarara ya yi amfani da matar aure mai shekaru 20, Maryam Muhammad, a bidiyon wakarsa mai suna JAHATA JAHATA TACE.

Ta kuma bayyana cewa wata kotun shari’a ta bukaci a binciki mawakin a kan haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel