Cin zarafi da rashawa na yan sanda a Najeriya: Rahoto

Cin zarafi da rashawa na yan sanda a Najeriya: Rahoto

- A baya-baya nan, hukumar yan sandan Najeriya ta fuskanci kalubale masu dimbin yawa kan zargin cin zarafin mutane

- Saura kiris zanga-zangar EndSARS da aka gudanar a watan Oktoba ta kifar da kasar nan

- Hukumar yan sanda ta lashi takobin cewa ba zata sake bari a gudanar da irin wannan zanga-zanga ba

Najeriya, a watan Oktoba, 2020 ta cakume da wani rikici da ya kusa durkusar da kasar yayinda akayi rashin rayukan da dukiya.

Abinda ya samo asali daga zangan-zangan lumana, ya canza zani zuwa rikici tsakanin jami'an tsaro da jama'a inda aka kwashi kwanaki babu doka, babu oda a Najeriya.

An budewa masu zanga-zangan lumana wuta, an hallaka jami'an yan sanda da iyalansu, an kona ofishohin yan sanda kuma an yi sace-sace a kantunan daidaikun mutane,

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa dukkan hakan ya faru ne sakamakon cin zarafi da yan sanda ke yiwa jama'a da rashawa; kuma wannan ya zama mugun cuta wacce ta kusa ko ina cikin lamarin tsaro da cigaban Najeriya.

Cin Zarafi da yan sanda ke yi

A ranar 3 ga Oktoba, matasa a fadin Najeriya sun fito kwansu da kwarkwatansu domin gudanar da zanga-zanga mai take '#EndSARS' domin kira ga kawo karshen wani sashen yan sanda mai suna SARS, wanda a cewar matasan sun shahara da kisan mutane ba gaira ba dalili.

A cewar rahoton Nairametrics, an kwashe kwanaki 21 ana wannan zanga-zanga kuma an yi asaran rayuka da dukiya.

Bayan zanga-zanga, mun zauna da wani Sufritandan na yan sanda wanda ya kwashe sama da shekaru 20 a aikin. Wanda ya bukaci a sakaye sunansa domin tsoron abinda ka iya biyo baya, domin sauraron na bakinsa da kuma gaskiyan zargin da ake yiwa yan sanda.

Yayinda muka tambayesa kan zargin cin zarafi da ake yiwa yan sanda, ya tabbatar da cewa lallai abokan aikinsa na aikata hakan amma ya ce mutanen Najeriya ne suka maishesu haka, saboda ba'a musu adalci.

Ya kara da cewa rashin isassun kayan aiki wajen gudanar da ayyukansu na cikin dalilan da ya sa suke zafi, saboda su kansu ba sa cikin farin ciki.

"Cin zarafin mutane bai cikin aikin yan sanda, amma al'ummar ce ta maishe mu azzalumai. Ba a yi mana adalci, kuma al'umma na samun irin yan sandan da suka cancanta," ya ce.

"Wani dalilin da ya sa muke hakan shine rashin isassun kayan aiki. Ba a bamu abubuwan da muke bukata. Muna da matsalan rashin kayan haka, muna da matsalan albashi, kuma hakan ke sa mu fushi da bacin rai."

Mun sake zama da wani jami'in dan sanda wanda ya ce wannan watan Nuwamban shekaru 20 da shiga aikin yan sanda, shi ma ya bukaci a sakaye sunansa. Ya ce ba kowani dan sanda ke da halin cin zarafi ba.

"Ni abinda na fahimta da cin zarafi shine kawai halin mutum ne." yace.

Bayan haka, mun samu rahotannin wasu mutane da yan sanda suka ci zarafinsu. Daga wadanda aka hallaka har lahira, zuwa wandanda aka azabtar.

Jaridar Punch ta ruwaito wata mata wacce tayi bayanin yadda yan sanda suka hallaka mata 'danta a unguwar Somolu na jihar Legas.

"An hallaka min dan shekara 20. Sun hana ni cin amfanin 'da na. Gwamnati ta fito da wadanda suka kashe min yaro ko kuma ta hukunta su," ta fadi.

Kalli cikakken bidiyonta a nan:

Bayan haka, wani matashi Ogan @OIrukwu, ya daura bidiyon News Central da ke nuna yadda wasu jami'an yan sandan suka doki wani mutumi don yayi magana yayinda ya ga wasu yan sanda na kokarin cin zarafin dan acaba.

Mutumin ya bayyana cewa bai fadi wani magana mai tsauri ba amma an buge sa.

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

Cin zarafi da rashawa na hukumar yan sanda a Najeriya a Najeriya: Rahoto
Cin zarafi da rashawa na hukumar yan sanda a Najeriya a Najeriya: Rahoto Hoto: Presidency
Source: Twitter

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai wa dakarun soji hari, sun kashe sojojin ruwa 2

Yan sanda da karban cin hanci da rashawa

Wani sakamakon bincike a kungiyar SERAP ta saki a watan Maris 2019 ya nuna cewa tsakanin 2014 da 2019, hukumar yan sanda ce hukuma mafi ta'amuni da rashawa cikin hukumomin gwamnatin Najeriya.

Sauran ma'aikatun da yan Najeriya suka bayyana ra'ayoyinsu kai sune bangaren wutan lantarki, bangaren sharia, Ilimi, da lafiya.

A cewar rahoton binciken, "kashi 54 na mutanen da suka gamu da yan sanda sun biya cin hanci. Binciken ya nuna cewa sau biyu cikin uku, dan sanda zai bukaci cin hanci daga hannun dan Najeriya a duk lokacin da suka hadu."

Hakazalika, mun zanta da ASP Maka (Ba sunansa na gaske ba), ya tabbatar mana da cewa lallai yan sanda na karban cin hanci hannun mutane, amma kuma yace babu yadda suka iya ne.

"Ba a bamu abubuwan da muke bukata, albashin bai kai mana ko ina, muna da matsalar masauki. Muna rashin abubuwa da yawa, ko kudin da ake ikirarin an saka mana a kasafin kudi, gwamnatin tarayya ba ta bamu," yace.

"Ko takardu ba a bamu, mu muke saya da kanmu. Yawancin lokuta da motocin kanmu muke amfani. Najeriya ce ta zamar damu masu rashawa."

Wani jami'in dan sanda, wanda ya bukaci a sakaye sunansa saboda tsoro ya bayyana mana cewa ko kayan aiki da kansu suke dinkawa.

"Shin ka san tun lokacin da na shiga aikin dan sanda a 1 ga Nuwamba 2000, kaya daya aka bani har yanzu, shekaru 20 kenan," ya ce.

Bayan haka, mun tattauna da direba, Usman, wanda yayi ikirarin yan sanda sun taba kwace masa kudi ba tare da ya aikata wani laifi ba.

"Sun gan ni ina hanyar tafiya Asokoro, suka ce in tsaya.... sai suka tambayeni katin lasisin tukin mota... sun duba takardu ne suka ce akwai wanda babu, mai suna 'takardar hujjan mallakin mota.', nace musu inada shi. sai suka tambayeni ina na samu kudin siyan mota, nace musu ni dan kasuwa ne," cewar direba, Usman.

"Sun ce tun da ban son fada musu gaskiya, zasu tafi da ni ofishinsu tare da wasu da suka kama. Yayinda muke hanyar tafiya, sun amsa kudi hannun sauran kuma suka sakesu. Amma tun da nace musu ban da kudi, sun kai ni ofishinsu kuma suka bukaci in biya N10,000."

"A karshe na biyasu N5000."

Ya bayyana yanzu cewa akwai bukatar gyara cikin hukumar yan sanda kuma akwai sauran aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel