Mawakin Buhari Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa

Mawakin Buhari Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa

- Mawakin siyasan nan mazaunin Kano, Rarara, ya sha caccaka a baya-bayan nan kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa

- A cewar rahotanni, an yi amfani da wata matar aure mai shekaru 20, Maryam Muhammad, a daya daga cikin bidiyon wakokinsa

- Mijin matar ya shigar da wata kara inda yayi zargin cewa ta hada kai da Rarara

A kwanan ne wata kotu ta bukaci a binciki shahararren mawakin siyasan nan mazaunin Kano, Dauda Kahutu Rarara, bayan ikirarin cewa ya yi amfani da matar aure a daya daga cikin bidiyon da ya saki a kwanan nan.

A cewar rahotanni daga jaridar The Guardian, an yi zargin cewa Rarara ya yi amfani da matar aure mai shekaru 20, Maryam Muhammad, a bidiyon wakarsa mai suna JAHATA JAHATA TACE.

Ta kuma bayyana cewa wata kotun shari’a ta bukaci a binciki mawakin a kan haka.

Mawakin Buhari Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa
Mawakin Buhari Rarara ya shiga matsala kan sanya matar aure a bidiyon wakarsa Hoto: @real_rarara_multimedia
Source: Instagram

KU KARANTA KUMA: An nemi Bala Mohammed ya shiga tseren shugaban kasa a 2023

An tattaro cewa mijin Maryam, Abdulkadir Inuwa, ya shigar da kara da kuma ikirarin cewa mawakin ya hade da matarsa a sirri.

Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa Maryam ta watsar da mijinta a gidansa jim kadan bayan aurensu kawai sai ya gano ta a bidiyon wakar mawakin.

Alkalin, Sarki Yola, ya kuma bayyana cewa ikirarin mawakin na cewa bai san Maryam matar aure bace bai isa a yi watsi da karar wanda Inuwa ya shigar ba. Sai dai ya umurci yan sandan da ya bincike lamarin sannan su gabatarwa da kotu sakamakon bincikensu.

Alkalin ya kuma bukaci yan sanda akan su aika sammaci ga mawakin da furodusansa don binciken lamarin.

A wani labari na daban, Allah ya yiwa shahararren malamin nan na addinin Musulunci da ke Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu rasuwa.

Shehin malamin ya rasu ne a safiyar yau Alhamis, 24 ga watan Disamba a garin Minna, babbar birnin jihar Niger.

Ya rasu yana da shekara 91 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel