An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

- Ta tabbata yanzu, annobar korona ta sake waiwaye a karo na biyu a Najeriya

- Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa dss

- An sake dokar kulle a jihar Kwara amma Plateau ta ce ba zata rufe jama'a ba

Alkaluma akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Mutane 1133 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 80,9222 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,274 yayinda 1236 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Korona 2.0: Babu sabuwar dokar kulle, Lai Mohammed

An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba
An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba Credit: @NCDCgov
Asali: Twitter

Ga jerin jiha-jiha:

Lagos-397

FCT-357

Kaduna-81

Plateau-63

Katsina-46

Sokoto-32

Oyo-28

Ogun-21

Kano-19

Rivers-18

Osun-13

Edo-12

Niger-12

Bayelsa-11

Borno-11

Bauchi-8

Jigawa-2

Ondo-2

KU KARANTA: Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu a cikin shugabannin LGAs na Borno

A bangare guda, Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyanawa majalisar dattawa cewa gwamnatin tarayya na bukatar N400bn domin siyawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona.

Ya bayyana haka ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na shirye da sayan rigakafin COVID-19 domin ceton rayuka amma ana bukatar N400 billion domin sayan rigakafin kashi 70 na al'ummar Najeriya milyan 200 akan farashin $8 ga kowani mutum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel