Nima yajin aikin ASUU ya shafi yaran cikina 3, Minista Ngige

Nima yajin aikin ASUU ya shafi yaran cikina 3, Minista Ngige

- Minista kwadago ya bayyanawa yan Najeriya shi mai kishin kasa ne

- Ya ce har wasu mambobin kungiyar ASUU ya fi kishi saboda makarantun kudi suka sanya yaransu ba na gwamnati

Ministan kwadago da daukan aiki, Chris Ngige, ya lashi takobin tabbatar da cewa kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU bata sake zuwa yajin aiki ba.

Ministan wanda ya lashi takobin haka a hirarsa da tashar Channel TV ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, ta ce yaransa uku na gida kuma yajin aikin ya shafesu.

Ya kara da cewa biyu cikin wadannan yaran nasa a Amurka aka haifesu kuma yana da daman kaisu can suyi karatu kyauta, amma bai yi hakan ba.

Ngige yace: "Ba san sake baiwa ASUU daman zuwa yajin aiki. Saboda ina da yaran cikina uku da suka wahala da wannan halin da muka samu kanmu ciki harda da kuma yara 15 da nike daukar nauyinsu a jami'o'in Najeriya."

"Ina da yara uku dake karatu a jami'o'in Najeriya. Ko sakandare a nan sukayi. Biyu cikinsu haifaffun Amurka ne kuma ina da daman kaisu Amurka karatu kuma kyauta ma, amma ban yi haka ba."

"Saboda haka ni mahaifi ne na kwarai, da ni ake damawa, kai na fi wasu mambobin ASUU kishi saboda 'yayansu makarantun kudi suke zuwa."

KU DUBA: A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

Kalli bidiyon nan:

KU KARANTA: An kuma, sama da mutane 1100 sun kamu da cutar Korona ranar Laraba

Jiya mun kawo muku cewa kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja.

Sanarwan ya biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren Talata.

Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da sharadin gwamnati ta cika alkawuranta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel