A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

- Mahaifin dalibar makarantar Dapci ya kai koke wajen gwamatin tarayya

- Tun shekarar 2018 da aka sako kawayenta, har yanzu babu labarin halin da take ciki

- Gwamnati ta samu nasarar ceto sama mata 100 cikin daliban Dapchi a watan Maris, 2018

Leah Sharibu na 'yar shekara 14 lokacin da yan ta'addan Boko Haram suka saceta ranar 19 ga Febrairu, 2018, tare da kawayenta 110 a makarantarsu, GGSS Dapci dake karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.

Tun daga lokacin ta kasance a hannunsu saboda ta ki amincewa ta canza addininta.

Mahaifinta, Nathan, wanda yayi magana da manema labarai ranar Talata, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka ta ceto diyarsa bayan shekaru uku hannun yan ta'addan, Vanguard ta ruwaito.

"Muna sake roko, muna rokon hukumomi su taimaka su ceto diyata. Na yi imanin zai yiwu saboda kwanan nan aka ceto dalibai a jihar Katsina," mahaifin ya bayyana.

"An bar mu cikin bakin ciki na tsawon shekaru uku yanzu, tun lokacin da aka sace Leah. Na san gwamnati sun yi mana alkawura da yawa amma har yanzu diyata na cikin daji."

"Wannan shine Kirismetinta na uku tun lokacin da aka saceta a Dapchi, amma muna sa rai."

KU KARANTA: Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa

A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kanaka, mahaifin Leah Sharibu
A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kanaka, mahaifin Leah Sharibu Hoto: Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

A wani labarin kuwa, wani mutumin jihar Michigan a kasar Amurka, ya samu yanci bayan kwashe kimanin shekaru 40 a gidan yari kan laifin da bai aikata ba.

A cewar CNN, mutumin mai suna Walter Forbes ya samu yanci ne bayan matar da tayi shaida kansa ta janye maganarta saboda karya tayi.

Walter Forbes, wanda ke da shekaru 63 yanzu, ya shiga kurkuku ne yana dalibin jami'a mai shekaru 25, bayan zarginsa da kisan Dennis Hall, a shekarar 1982, ABC ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel