Yanzu-yanzu: Bayan watanni 9, ASUU ta janye daga yajin aiki

Yanzu-yanzu: Bayan watanni 9, ASUU ta janye daga yajin aiki

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja.

Sanarwan ya biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren Talata.

Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da sharadin gwamnati ta cika alkawuranta.

Muddin gwamnati ta saba, a cewarsa, zasu koma yajin aiki ba tare da sanarwa ko talala ba.

Yayinda aka tambayesa shin an fara biyansu albashinsu da suke bi, ya ce an fara biyansu amma ba'a gama ba.

Ya jaddada cewa ba dan rashin albashi suka tafi yajin aiki ba.

KU DUBA: A ceto min diyata kaman yadda aka ceto daliban Kankara, mahaifin Leah Sharibu

Yanzu-yanzu: Bayan watanni 9, ASUU ta janye daga yajin aiki
Yanzu-yanzu: Bayan watanni 9, ASUU ta janye daga yajin aiki
Source: Original

KU KARANTA: Mutumin da ya kwashe shekaru 40 a kurkuku ya samu yanci bayan wacce tayi shaida kansa a kotu tace karya tayi masa

A baya mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'ar da ta gabata, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

Yayin karanto abubuwan da suka tattauna bayan sa'o'i bakwai ana tattaunawa a dakin taron ma'aikatar kwadago, Ministan, Chris Ngige, ya ce gwamnati ta amince a biya mambobin ASUU albashinsu tun daga watan Febrairu zuwa Yuni da tsohon manhajar GIFMIS.

Hakazalika gwamnatin ta amince da kara kudin alawus na malaman daga N30bn zuwa N35bn, sannan kudin gyaran jami'o'i daga N20bn zuwa N25bn.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel