Da duminsa: FG ta bada hutun Kirsimeti da Sabon shekara

Da duminsa: FG ta bada hutun Kirsimeti da Sabon shekara

- Gwamnatin tarayya ta bada hutun bukukuwar Krsimeti, Ranar bada kyaututuka (Boxing Day), da kuma sabon shekara

- Ranakun hutun sune Juma'a 25 da Litinin 28 ga watan Disambar 2020, sai kuma ranar Juma'a 1 ga watan Janairun 2021

- Gwamnatin ta janyo hankulan 'yan Najeriya kan darrusan da bukukuwan suka kunsa tare da shawartarsu su kiyaye dokokin yada korona

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma'a 25 ga wata da Litinin 28 ga watan Disamban 2020 da Juma'a 1 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranakun hutu don bikin Kirsimeti, Boxing Day da kuma Sabon shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwar da sakataren dindindin na ma'aikatar Dakta Shuaibu Belgore ya rattaba hannu a kai a ranar Laraba.

Da duminsa: FG ta bada hutun Kirsimeti da Sabon shekara
Da duminsa: FG ta bada hutun Kirsimeti da Sabon shekara. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: APC na Kano ta yi wa Kwankwaso martani, ta ce 'za mu murde zaben kuma ba abinda zai faru'

A yayin da ya ke taya kiristan Najeriya da na kasashen waje murnar bikin Kirsimetin da Sabon shekara, Aregbesola ya bukaci kiristoci su yi koyi da koyarwar Annabi Isa da suka hada da imani da kauna.

"Ya zama dole muyi koyi da rayuwar kankan da kai, hidima, tausayi, hakuri, zaman lafiya da tsoron Allah da Annabi Isah (AS) ya siffantu da su, wannan shine hanya mafi dacewa da za mu yi murnar zagoyowar ranar haihuwarsa," in ji shi.

Ya bayyana cewa zaman lafiya da tsaro abubuwa ne da ke da muhimmanci da za su bawa gwamnati daman farfado da tattalin arziki, janyo hankulan masu saka hannun jari da samar da ayyuka da miliyoyin matasan Najeriya cikin shekaru 10 masu zuwa.

Aregbesola ya kuma janyo hankulan 'yan Najeriya su cigaba da bin dokokin hukumomin lafiya da gwamnati na kare yaduwar annobar corona da ta dawo a karo na biyu musamman a lokaci irin na bukukuwa.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP a Ondo ta dakatar da jiga-jigan mambobinta biyar

Ministan ya ce gwamnati zata cigaba da iya kokarinta don ganin ta kawar da yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifuka a kasar yayin da ya bukaci yan Najeriya su cigaba da hakuri.

A wani rahoton daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel