An damke Uba, 'da, da jika kan laifin kisan mutane 2 a jihar Kano

An damke Uba, 'da, da jika kan laifin kisan mutane 2 a jihar Kano

- Yan gida daya sun hallaka wanda suke zargi da laifin garkuwa da mutane

- Bayan sama da watanni uku da aikata laifin, yan gidan sun shiga hannun hukuma

Jami'an hukumar yan sanda a jihar Kano sun damke wani mutumi mai suna, Adamu Musa, 'dansa, sule Mallam, da jikansa, Isyaku sule, kan laifin kisan wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane.

Ba shi kadai suka kashe ba, sun hada da diyarsa mai shekaru biyar da haihuwa, Premium Times ta ruwaito.

Wannan abu ya auku ne a kauyen Gomo, a karamar hukumar Sumaila a jihar Kano.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana a ranar 26 ga Agusta cewa sun dira gidan mutumin mai suna Kabiru Yau, dake Madunkuri a garin Gomo kuma suka kashehi da diyarsa, Harira Yakubu.

Kakakin a jawabin da ya saki ranar Talata ta ce Malam Musa ya amsa laifin hannu cikin kisan kai.

Yace "ya umurci yaransa uku da jikansa su kashe mutumin kan zargin cewa yana garkuwa da mutane."

Sun yi amfani da adduna da gorori wajen dukan mutumin da diyarsa har lahira, a cewar Kiyawa.

Ya kara da cewa an damkesu ne ranar 19 ga watan Disamba, kimanin kwanaki 119 bayan da suka aikata laifin kisan.

KU KARANTA: Bayan watanni 9, ASUU ta janye daga yajin aiki

A Kano: An damke Uba, Yaronsa da jikansa kan laifin kisan mutane 2
A Kano: An damke Uba, Yaronsa da jikansa kan laifin kisan mutane 2 Credit: https:/www.premiumtimesng.com
Source: UGC

KU KARANTA: Kuma dai! Kimanin mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

A bangare guda, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a daren ranar Litinin, sun yi garkuwa da hakimin kauyen Kaigar Malamai, a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina tare da wasu mutum 15.

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa yan bindigan su da yawa sun kai farmaki kauyen da misalin tsakar dare a ranar Litinin sannan suka shafe tsawon sa’o’i da dama suna aiki inda daga baya suka tafi da mutanen.

“Sun kai farmaki kauyenmu, Unguwar Malamai da misalin karfe 11:45 na tare sannan suka fara harbi ba kakkautawa." yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel