Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina

- Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kaigar Malamai da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina

- Maharan sun kuma yi garkuwa da Hakimin kauyen, matan aure, yan mata da kuma wasu kananan yara

- Zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin yan sanda game da lamarin ba

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a daren ranar Litinin, sun yi garkuwa da hakimin kauyen Kaigar Malamai, a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina tare da wasu mutum 15.

Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa yan bindigan su da yawa sun kai farmaki kauyen da misalin tsakar dare a ranar Litinin sannan suka shafe tsawon sa’o’i da dama suna aiki inda daga baya suka tafi da mutanen.

KU KARANTA KUMA: Daga karshe fadar Shugaban kasa ta bayyana wadanda suka taimaka wajen sakin yaran Kankara

Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina
Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 15 a kauyen Katsina Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

“Sun kai farmaki kauyenmu, Unguwar Malamai da misalin karfe 11:45 na tare sannan suka fara harbi ba kakkautawa.

“Sun yi garkuwa da mutum 16 ciki harda hakimin kauyen, Maiunguwa Kabir, matan aure shida, yan mata uku da kuma yara shida,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, bai rigada ya tabbatar da lamarin ba amma ya yi alkawarin dawowa ga manema labarai wanda hakan bai samu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Mun gano ana shirin saka Bam lokacin Kirismeti, Hukumar DSS

A wani labarin, wani jami'in dan sanda kuma dogarin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane amma ya samu kubuta.

Dan sandan, wanda dan asalin jihar Nasarawa ne, yana kan hanyar zuwa Abuja daga Doma a karshen makon da ya gabata akayi garkuwa da shi a Ikari, wani kauye dake Gudi karkashin karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.

Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na dare yayinda yan bindigan suka tare hanya, suka yi fashi, sannan sukayi awon gaba da mutane hudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng