Kuma dai! Kimanin mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

Kuma dai! Kimanin mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar Talata

- Ko shakka babu yanzu, annobar korona ta sake yunkurowa a karo na biyu

- Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa dss

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.

Mutane 999 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 22 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 79,789 a Najeriya.

Daga cikin kimanin mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 68,879 yayinda 1231 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar

Kuma dai! Kimanin mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar Talata
Kuma dai! Kimanin mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar Talata Credit: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU DUBA: Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

Ga jerin wadanda:

FCT-416

Lagos-324

Kaduna-68

Plateau-42

Kwara-32

Kano-24

Gombe-14

Sokoto-12

Yobe-12

Akwa Ibom-11

Bayelsa-10

Rivers-7

Bauchi-7

Ogun-6

Oyo-5

Edo-4

Taraba-4

Jigawa-1

A bangare guda, yayinda ake tsoron sake kakaba dokar kulle karo na biyu a fadin Najeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana Legas, Kaduna da Abuja matsayin manyan cibiyoyin kamuwa da Korona.

Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayya, ya bayyana hakan ranar Litnin, 21 ga Disamba, a Abuja yayin hira da manema labarai, ThisDay ta ruwaito.

A cewar shugaban kwamitin PTF, wadannan jihohin ne suka kwashi kashi 70% na adadin masu Korona a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng