PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP

PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP

- Hukumar kula da aikin 'dan sanda (PSC) ta amince da sallamar wasu manyan jami'an rundunar 'yan sanda daga aiki

- PSC ta sanar da cewa ta sallami jami'an daga aiki ne bayan samunsu da aikata laifuka daban-daban da suka sabawa aikin dan sanda

- Daga cikinsu akwai jami'an ada aka samu da laifin safarar muggan makamai zuwa cikin Nigeria

Hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC) ta sanar da sallami wasu manyan jami'an rundunar 'yan sanda guda huɗu bisa laifukan da suka shafi cin amana da nuna rashin kwarewa a aiki.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar tare da aika sako zuwa ga manema labarai a yau, Lahadi, a Jihar Lagos, kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Mr Ani ya ce, hukumar ta ɗauki wannan mataki yayin wani zaman ganawa da hukumar ta yi ranar Juma'ar da ta gabata.

An sallami babban Sufuritanda (CSP) na 'yan sanda bisa rashin gaskiya da nuna halayen da suka da na jami'in tsaro.

KARANTA: CBN za ta fara rabawa masu kiwon kaji da tsuntsaye tallafin biliyan N12.8

"Sannan an kara sallami wani jami'in dan sanda mai mukamin Sufuritanda (SP) bayan samunsa da laifin haɗa baki tare da wasu batagari guda hudu domin sace na'urar rarraba hasken wutar lantarki a unguwa; wato taransifoma.

PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP
PSC ta kori manyan 'yan sanda hudu daga aiki; CSP, DSP 2, da ASP
Asali: Getty Images

"Kazalika, PCS ta bayar da umarnin a gurfanar da shi saboda rasin gaskiyar da ya nuna da kuma cin amanar aikin dan sanda.

“Sai kuma karin wasu manyan jami'an guda biyu da suka hada da babban mataimakan sufuritanda (DSP) da mataimakin Sufuritanda (ASP), a cewar Ani.

KARANTA: Dawowar korona: El-Rufa'i ya sake daukan mataki da ya shafi wasu ma'aikata, Masallatai da Cocinan jihar Kaduna

Ani ya kara da cewa; “mataimakin Sufuritandan (ASP) ya jagoranci shigo da makamai ta barauniyar hanya daga kasar Benin.

"Shi kuwa DSP an same shi da laifin fitar da wasikar bogi domin rakiyar wata kwambar motocin SARS da zummar an sake su ne a hukumance.

"Sa'ar da aka yi lokacin sojoji na kan aikin bincike kan hanyar da suka je wucewa, suka binciki kayan dake cikin motocin. DSP din da abokan laifinsa sun tsere, sun bar motocin a nan."

Ani ya tabbatar da cewa kowanne cikin su zai fuskanci fushin hukuma.

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'adddanci a duniya ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello.

Kotun ta shawarci Jastis Bello, dan takarar Nigeria da Buhari ya zaba, bayan ya samu kuri'u a zagayen zabe na farko da kuma samun kuri'u a zagaye na biyu na zaben.

ICC za ta zabi sabbin alkalai 6 ne daga cikin jimillar alkalai 18 da kotun, wacce ke kasar Geneva Switherland, ya kamata ta mallaka.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel